Sojojin Najeriya sun ceto 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya da Boko Haram ta yi awon gaba da su.
Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya tabbatarwa BBC cewa sojojin Najeriya sun bi 'yan Boko Haram tare da kwato daliban.
Ya ce yanzu haka 'dalibai matan suna hannun sojojin da suka kwato su, kuma nan gaba gwamnatin Yobe za ta yi karin bayani.
Yadda wata 'yar Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram
Nigeria:'Yan matan Chibok za su koma wurin iyayensu
A ranar Litini ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari makarantar inda suka yi ta harbe-harbe tare da tayar da abun fashewa.
Rahotanni sun ce maharan sun sace kayayyaki daga makarantar bayan sun tarar wasu daliban da malaman sun tsere
Source :bbc hausa
Title :
Anceto Yanmatan Da Aka Sace A Yobe
Description : Sojojin Najeriya sun ceto 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya da Boko Haram ta...
Rating :
5