Yan sanda sun kwantar da tarzomar da ta taso tsakanin musulmi da kirista, sakamakon musuluntar da wata matashiya ta yi a kasuwar magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Tun da fari an kona gidaje bayan barkewar rikici, kuma mutane 12 aka tabbatar da mutuwarsu.
Lamarin ya samo asali ne bayan wata matashiya ta musulunta, sai 'yan uwanta suka ce sam ba su amince da hakan ba, ba tare da bata lokaci ba sai matashiyar ta hada kayan ta tabar musu gidan.
Rahotannin da muka samu sun ce, matashiyar na soyayya tsakanin ta da wani musulmi, inda kiristoci suka bukaci duk wata da ke son musulmi ta daina.
Kuma Kiristocin sun bukaci duk macen da ta yi aure a gidan musulmi ta fita ko su fitar da ita da karfi.
A jiya litinin kuma wasu matasa sun fantsama cikin gari inda rikici ya kaure.
'Yan sanda ba su bayyana mutanen da suka rasu ba, amma hausawa mazauna garin sun ce sun kirga gawarwakin mutanen 12 yayin da suka ce ana ci gaba da tattara gawarwakin wadanda suka mutu.
Me ya sa El-Rufai ya rusawa Hunkuyi gida a Kaduna?
Nigeria: Zaki ya kashe mai kula da shi a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da al'amarin, inda ta bayyana cewa ta tura jami'an tsaro domin magance rikicin da ruruwarsa.
Sai dai a cikin sanarwar da Samuel Aruwan kakakin gwamnan Jihar Kaduna ya fitar bai fadi adadin mutanen da suka mutu ba da adadin wadanda suka jikkata.
Sanarwar ta ce gwamnan Jihar Malam Nasir El Rufa'i ya umurci jami'an tsaro su gudanar da bincike tare da kame duk wadanda ke da hannu a rikicin da ya faru a Kasuwar Magani.
Tazarar nisan kilomita 31 ne tsakanin Garin Kasuwan Magani da birnin Kaduna.
Source :bbc hausa
Title :
An Kwantar Tarzoman Data Taso A Kaduna
Description : Yan sanda sun kwantar da tarzomar da ta taso tsakanin musulmi da kirista, sakamakon musuluntar da wata matashiya ta yi a kasuwar magani da k...
Rating :
5