A Najeriya, kwana biyar bayan 'yan bindiga da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai hari kan wata makarantar mata a garin Dapchi na jihar Yobe, an fitar da sunaye dari da biyar da aka ce na dalibai mata da ba a gani bane sakamakon harin.
A ranar Juma'a ne gwamnatin jihar Yobe ta ce adadin daliban da ba a gani ba, tamanin da hudu ne.
Mako guda kenan da ake ci gaba da samun bayanai da suka sha banban, da kuma rudani daga hukumomi, dangane da adadin dalibai mata da aka yi gaba da su daga makarantarsu a Dapchi.
A karon farko, iyayen 'yan matan sun fitar da jerin sunayen 'ya'yansu da har yanzu ba a gani ba.
Sunaye dari da biyar ne iyayen 'yan matan suka fitar.
Tun da farko dai, gwamnatin jihar ta ce daliban hamsin da daya ne ba a gani ba, sannan daga baya ta ce adadin daliban da ba a gani din ba tamanin da hudu ne.
An ce 'yan matan sun gudu ne zuwa cikin daji a lokacin da aka kai wa makarantar ta su hari.
Sai dai da yawa daga cikin 'yan matan ba su koma gida ba, abin da yasa iyayensu suka shiga fargabar ko an sace su ne.
A ranar Juma'a, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani bala'i da ya samu kasar, sannan ya ce sojoji suna yin komai domin gano 'yan matan.
Halin da ake ciki a Dapchi, ya sa sace dalibai mata 276 da 'yan bindiga suka yi a 2014, dawowa zukatan mutane.
Source :bbc hausa
Title :
An fidda sunayen dalibai 105 da akayi awun Gaba Dasu a Dapchi
Description : A Najeriya, kwana biyar bayan 'yan bindiga da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai hari kan wata makarantar mata a garin Dapchi na j...
Rating :
5