Yakubu Dogara, Kakakin majalisar wakilai ya bayyana cewa, babban kalubalen dake kan kungiyar kwadago a halin yanzu shine ta nemi sasanci kan mafi karancin albashin ma'aikata a kasar nan.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne da sanadin mai magana da yawun sa, Turaki Hassan, a ranar tunawa da kafuwar kungiyar shekaru 40 da suka gabata.
Dogara ya yabawa ƙarfin hali na kungiyar dangane da yadda take fafutikar kwato 'yancin dukkan ma'aikata dake fadin kasar nan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a wasu lokuta hukumar ta kalubalanci hukumomin tsaro wajen gudanar da yajin aiki a matsayin barazana wajen neman janyo hankalin gwamnati.
Source :naij hausa
Title :
Akwai Babban Kalubale Akan Kungiyar Kwadago-Dogara
Description : Yakubu Dogara, Kakakin majalisar wakilai ya bayyana cewa, babban kalubalen dake kan kungiyar kwadago a halin yanzu shine ta nemi sasanci kan...
Rating :
5