Wani malamin addinin Kirista, Bishop Sam Zuga, ya bayyana cewar addinin musulunci gaba yake da na Kiristanci bisa dogaro da wasu hujjoji.Malamin addinin ya bayar da hujjojin kamar haka:
An haifi Annabi Isa (AS) shekaru 571 kafin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) amma duk da haka addinin musulunci na goga kafada da Kiristanci.
Musulumi na yin sallah biyar a rana amma da kyar kiristoci ke zuwa coci sau daya a sati.Ya kara da cewar Qur'an guda daya ne kuma cikin yare guda amma littafin injila (bibble) ya fi kashi 10 a cikin yaren Turanci kadai.
Musulumi kan iya yin sallah a kowanne masallaci kuma a ko ina amma mabiya addinin Kirista ba zasu soma shiga wata cocin ba saboda ba a irinta su ke ibada ba.Idan har karbi addinin musulunci, babu mai tambayar ka masallacin ka, amma idan mutum ya zama Kirista dole sai ya zabi coci ko kuma ka tashi a tutar babu.
Musulumi sun fi kiristoci saukin kai domin sun sha halartar tararruka na a garin Gboko, jihar Benuwe, wani abu da Kiristoci ba zasu iya ba.Akwai yarda wurin musulmi domin da zarar mutum ya karbi addinin musulunci zaka ga kowa na son taimakon shi.
Bishop Zuga ya kara da cewar babu rarrabuwar kai tsakanin musulmi kamar yadda ake samu a Kiristanci domin idan ba ka yi bincike ko ka zauna da musulmi ba, ba lallai ka san akwai rabuwar kai tsakaninsu ba.
Source :naij hausa
Title :
Abunda ya sa addinin musulunci ya fi na Kiristanci - Bishop Sam Zuga
Description : Wani malamin addinin Kirista, Bishop Sam Zuga, ya bayyana cewar addinin musulunci gaba yake da na Kiristanci bisa dogaro da wasu hujjoji.Mal...
Rating :
5