Crystal Palace ta kawo karshen lashe wasa 18 a jere da Manchester City ta yi a jere a gasar Premier ta shekarar nan.
Manchester City da Crystal Palace sun tashi wasa babu ci a karawar mako na 21 da suka yi a ranar Lahadi.
Daf da za a tashi daga kwallo Palace ta samu bugun fenariti bayan da Raheem Sterling ya yi wa Wilfred Zaha keta a yadi na 18 din City.
Sai dai Palace din ba ta ci kwallon da Luka Milivojevic ya buga ba, inda mai tsaron ragar City, Ederson ya hana ta shiga gidan kifi.
Cikin wasa 21 da City ta buga a gasar Premier ta bana, ta ci wasa 19 inda 18 a jere ta yi nasara, sannan ta buga canjaras a fafatawa biyu a gasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Man City Takasa Cin Crystal Palace
Description : Crystal Palace ta kawo karshen lashe wasa 18 a jere da Manchester City ta yi a jere a gasar Premier ta shekarar nan. Manchester City da Cry...
Rating :
5