Dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema zai yi jinya, sakamakon raunin da ya ji a wasan hamayya da Barcelona wanda ake yi wa lakabi da El Clasico.
Real ba ta bayyana ranar da Benzema zai dawo fagen tamaula ba, bisa raunin da ya yi a kafarsa ta hagu ba.
Sai dai kuma ana rade-radin cewar dan kwallon ba zai buga wasan Copa del Rey da Real za ta yi da Numancia gida da waje da karawa da Celta Vigo a gasar La Liga da watakila fafatawa da Villarreal da kuma Deportivo La Coruna ba.
Benzema bai halarci atisayen da Madrid ta fara a ranar Asabar ba, sai da likitocin kungiyar sun duba girman raunin da ya yi a ranar 23 ga watan Disamba.
Real Madrid wadda ta ci kofi biyar a 2017, tana ta hudu a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu da Paris St Germain a gasar Zakarun Turai a watan Fabrairu.
Source: BBC Hausa
Title :
Karim Benzema Zaiyi Jinya
Description : Dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema zai yi jinya, sakamakon raunin da ya ji a wasan hamayya da Barcelona wanda ake yi wa lakabi da El Cla...
Rating :
5