China ta rage harajin shiga da fatar jaki kasar, wadda suke amfani da ita wajen hada maganin gargajiya, duk da tsoron da ake na rage yawan dabbobi a fadin duniya.
Daga ranar Litinin ne za a rage harajin daga kashi biyar cikin 100 zuwa kashi biyu cikin 100, don saukaka shiga da shi.
Maganin da ake yi da fatar jakin na da matukar tsada a kasar, kuma shi ne maganin da aka fi saye a shekarun baya-bayan nan.
Masu fafutuka sun ce hakan zai kawo rage yawan jakai a kasashen Afirka, inda aka fi yin amfani da su wajen daukar kaya da kuma tafiye-tafiye.
A yawancin kasashen Afirka, tuni aka samu karancin dabbobi sakamakon samun yawan bukatarsu.
A China kuwa ana amfani da fatar jakin ne wajen hada maganin gargajiya na gelatine, wanda yake maganin amosanin jini.
Har ila yau naman jaki shaharrren abinci ne a China, amma saboda karancinshi a kasar da kuma rashin yawan haihuwa akai-akai ya tilasta musu fita wasu kasashen nemo shi.
Ana amfani da dafaffiyar fatar jaki wajen hada magani Ejiao, inda suke sayer da shi kusan fam 300 duk kilo daya.
Tuni kasashen Afirka irinsu Uganda, daTanzania, da Botswana, da Niger, da Burkina Faso, da Mali, da kuma Senegal suka haramta fitar da jakai zuwa China.
Source: BBC Hausa
Title :
China Tarage Harajin Shigar Da Fatan Jaki Kasar
Description : China ta rage harajin shiga da fatar jaki kasar, wadda suke amfani da ita wajen hada maganin gargajiya, duk da tsoron da ake na rage yawan d...
Rating :
5