Ana ci gaba da gudanar da shagulgulan shigowar sabuwar shekarar 2018 a sassa daban daban na duniya tare da yin kiran kaucewa rikice-rikice a sabuwar shekarar.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce rikicin da aka fama da shi a sassa da dama na duniya ya yi kamari inda ake fuskantar sabbin barazana cikin watanni 12 da suka gabata.
A sakonsa na sabuwar shekara, Mr Guterres ya ce wariyar launin fata na karuwa a duniya kuma zaman zullumi kan barkewar yaki da makamin nukiya ya kai kololuwa tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka.
Ya ce a lokacin da ya kama aiki shekara guda kenan, ya yi roko akan Allah yasa shekarar 2017 ta zama shekarar zaman lafiya, amma sabanin haka duniya ta shaida.
A don haka sakon sa na sabuwar shekarar 2018 shi ne ankarar da duniya halin da ake ciki--rigingimu na kara kamari, kuma sabbin barazana sai bullowa suke yi.
A sakonta na murnar sabuwar shekara, Firai Ministar Burtaniya Theresa May ta ce 'yan kasar za su kara samun kwarin guiwa tare da alfahari a 2018.
Ta ce duk da cewa ficewar Burtaniya daga tarayyar turai ya na da muhimmanci a sabuwar shekarar, amma hakan bai takaita burin gwamnati ba na maida hankali don inganta rayuwar al'ummarta.
Shugaba Xi Jinping na kasar China ya ce duniya na shaukin ganin Beijing tana bayyana matsayinta karara kan batutuwan da suka shafi kasashen duniya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun yi magana akan karfafa danganta a tarayyar turai.
A sakon daya rubuta a shafin sa na Twitter, shugaba Donald Trump ya yi wa abokansa da magoya bayan sa fatan alheri a sabuwar shekara tare da yin kiran a yi watsi da labarai na boge a kafofin da ke watsawa;
A kasashen duniya da dama dai jama'a sun taru a tsakiyar biranen su musamman a nahiyar turai da wasu kasashen Afrika don murnar shigowar sabuwar shekara.
An dai tsaurara matakan tsaro a biranen Paris da London da kuma Berlin na kasar Jamus.
Source: BBC Hausa
Title :
Anci Gaba Da Murnar Shiga Sabon Shekara A Duniya
Description : Ana ci gaba da gudanar da shagulgulan shigowar sabuwar shekarar 2018 a sassa daban daban na duniya tare da yin kiran kaucewa rikice-rikice a...
Rating :
5