Tsawon Shekara Bakwai Yana Aiki A Matsayin Jami'in Kwastan, Amma Na Bogi
Jami'in kwastan din bogi a kasar Kwadebuwa, a kullum idan zai bar gida da zimmar zai tafi aiki, yakan sanya kaki, ya sabi bindiga daga nan kuma ya ce wa matarsa ta taya shi da addu'a zai fita aiki. Kafin daga baya dubunsa ta cika, inda yanzu haka yana tsare a hannun hukumar kasar ta Ivory Coast.