Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya, Idris Kpotun, ya bayar da umarnin a gyara fasalin rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da masu fashi da makami.
Wannan na zuwa ne a lokacin da 'yan Najeriya suka yi ta suka a shafukan sa da zumunta game da zargin rundunonin 'yan sanda masu yakar masu fashi da makami da cin zarafin al'umma.
Masu fafutika da masu ruwa da tsaki a lamarin dai sun yi ta amfani da maudu'in #EndSARs a shafin sa da zumunta na Twitter, domin kira da a kawo karshen rundunonin.
A ranar wata Asabar ce wani mai amfani da shafin sa da zumunta na Twitter @YabaKid, ya yi ikirarin cewa a gabansa wasu jami'an SARs suka harbi wani yaro a kansa.
Tun a lokacin yake wallafa sakonni a shafin na Twitter da maudu'in #EndSARS, wato a kawo karshen SARs tsawon watanni, amma sai a 'yan kwanakin baya-bayan nan ne dubban masu amfani shafin suka fara wallafa irin wadannan labaran, inda suke fadin yadda jami'an SARs din ke cin zarafin mutane.
Da yawa sun ce jami'an sun sha nuna musu bakin bindiga, ko kuma su kama su ba tare da wata tuhuma ba, su tilasta musu bayar da cin hanci, ko ma su harbe mutane.
Kiraye-kirayen ne suka sa Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya ba da umarnin yin garambawul a kan rundunar ta SARs, tare da yin bincike a kan dukkanin zarge-zargen.
Sannan rundunar ta fitar da lambobin wayoyi da adireshin email da wasu kafofin sada zumunta, inda ta bukaci mutane su kai kokensu na cin zarafin da suke zargin an yi musu, don a bincika tare da daukar matakan da suka dace.
A Najeriya dai an dade ana zargin cewa 'yan sanda suna cin zarafin mutane, zargin da 'yan sandan suke musantawa.
Source: BBC Hausa
Title :
Zaayi Wa Rundunar SARS Garanbawul
Description : Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya, Idris Kpotun, ya bayar da umarnin a gyara fasalin rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki d...
Rating :
5