Idan an jima a yau ne za a fara shari'ar magajin garin Dakar Khalifa Sall, na kasar Senegal.
Tun a ranar bakwai ga watan Maris din daya gabata ne ake tsare da magajin garin Dakar din, lokacin da alkalin da ke gudanar da bincike kan dala biliyan uku da suka yi batan dabo inda aka tuhume shi da almundahana da hada baki da kuma aikata laifin hallata kudin haram.
Sai dai ya musanta zargin da ake yi masa.
An dai kama shi ne tare da wasu mukarabansa su bakwai.
Lauyoyinsa sun dinga kokarin ganin cewa an bada belinsu, amma hakarsu bata cimma ruwa ba saboda alkalin ya ki ya amincewa da bukatar da suka shigar a gaban kotu.
Magajin jarin wanda dan jamiyyar Socalisat ne, ya gudanar da yakin neman zabensa a gidan yari a zaben majalisar dokokin da aka yi watan Yulin da ya gabata
Sai dai a watan Nuwamban daya gabata ne ya zama mamba a majalisar dokokin amma kuma gwamatin Senegal ta cire masa rigar kariyar da yake da ita a matsayinsa na mamba a majalisar dokoki.
Mr Sall, wanda shi ne magajin garin Dakar tun daga shekarar 2009, an rika masa kallon wanda zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za'a yi a shekarar 2019.
Sai dai magoya bayansa sun ce zargin da ake yi masa kan almundahana ba komai bane illa wani shirin da aka shirya domin ya kawo cikas ga anniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Idan kotu ta same shi da laifi, to watakila a yanke masa da kuma mukaranbansa hukuncin daurin shekara goma a gidan kaso.
Source: BBC Hausa
Title :
Zaa Fara Shariar Magajin Garin Dakar Kan Almundahana
Description : Idan an jima a yau ne za a fara shari'ar magajin garin Dakar Khalifa Sall, na kasar Senegal. Tun a ranar bakwai ga watan Maris din daya...
Rating :
5