Wani sabon rahoto ya ce yanayin rashin aikin yi ya kara tabarbarewa a Najeriya, inda marasa aiki suka kai miliyan 17 a bana daga miliyan 13 a 2016.
Rahoton, wanda Hukumar Kididdiga ta kasar NBS ta fitar, ya bayyana cewa tabarbarewar tattalin arziki da aka yi fama da ita zai iya zama babban abun da ya munana lamarin, kuma za a iya shafe shekara daya kafin yanayin ya sauya.
Ya kuma kara da cewa rashin aikin yi ya karu da kashi biyar cikin 100.
Rahoton ya yi hasashen cewa za a dauki tsawon wata hudu zuwa takwas ba tare da an samu sauyi ba, kafin tattalin arzikin kasar ya kara farfadowa.
Sharhi dags wakilin BBC Chris Eworkor
Ga alama wannan rahoto na bayyana abun da yake a zahiri ne.
Faduwar farashin man fetur da kuma rashin samun kudin shiga sun sa gwamnati na fafutukar ci gaba da biyan ma'aikatanta.
A yayin da ake samun sabbin wadanda suka kammala karatu masu neman aiki, a wannan lokaci ne kuma kamfanoni masu zaman kansu da masana'antu suke rage yawan ma'aikatansu.
Masana tattalin arziki sun yi imani cewa, karancin hada-hadar kasuwanci da kuma rasa ayyuka na nufin iyalai da dama na fafutukar yadda za su rayu.
Source: BBC Hausa
Title :
Yawan Marasa Aiki Sunkaru A Nijeriya-Rahoto
Description : Wani sabon rahoto ya ce yanayin rashin aikin yi ya kara tabarbarewa a Najeriya, inda marasa aiki suka kai miliyan 17 a bana daga miliyan 13 ...
Rating :
5