Dubban mutane sun gudanar da wata zanga-zanga a sassan Nijar domin adawa da wani kudirin gwamnati na karin haraji da zai fara aiki a badi.
Karin harajin ya shafi na gidaje da dukiyar gado a kasafin kudin kasar na 2018.
Haka kuma matakin ya shafi karin kudaden ruwa da lantarki tare da karin haraji ga harakokin kasuwanci.
Gwamnatin Nijar ta ce daukar matakin ya zama wajibi domin samun kudaden da za ta aiwatar da ayyukan ci gaba a fadin kasar.
Tuni dai Majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin kudin na badi.
Kungiyoyin fararen hula ne suka jagoranci zanga-zangar a sassan biranen Nijar, yayin da hukumomi suka haramta jerin gwanon a Yamai fadar gwamnatin kasar saboda dalilai na tsaro.
Wasu daga cikin 'yan Nijar da suka fito zanga-zangar sun shaidawa BBC cewa karin harajin zai kara jefa rayuwarsu cikin kunci tare da yin kira ga hukumomin kasar su jingine matakin.
Kungiyoyin fararen hular, sun shaida wa jama'a cewa kashi 94 cikin 100 na kasafin kudin a jikin talaka za a tatsa, yayin da ake sa ran samun kashi uku cikin 100 na kudaden daga albarkacin ma'adinan da kasar ke da su.
Nijar mai arzikin ma'adinin Uranium, na cikin kasashen da ke fama da talauci a duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Nijar Na Adawa Da Karin Haraji
Description : Dubban mutane sun gudanar da wata zanga-zanga a sassan Nijar domin adawa da wani kudirin gwamnati na karin haraji da zai fara aiki a badi. ...
Rating :
5