Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun zama abin nan da Hausawa ke cewa dankali sha kushe.
"Allah yana kallon abin da muke yi; idan muna yi don mu bata ko mu gyara mu fadakar, Allah ya sani.
"A cikin fina-finan da muke yi ana yin karatun Al-Qur'ani, ana jan baki a fassara, ana ce wa 'Allah ya ce, Annabi ya ce'. Shi ma duk wannan koya rashin tarbiyya ne?", in ji Hadiza, lokacin da take amsa tambayar da BBC ta yi mata kan zargin bata tarbiya da ake yi wa 'yan fim.
Ta kara da cewa: "Ka san mu dankali ne sha kushe, ana sonmu ana kushe mu. Amma haka za mu yi ta tafiya tun da haka Allah ya yo mu.
"Haka za a yi ta hakuri da mu, mu ma muna hakuri da masu kushe mu kuma a hankali za su fahimce mu. Na san wasu ma sun fahimta yanzu."
Jarumar, wacce akasari ta fi fitowa a matsayin uwa, ta kara da cewa ta soma sha'awar fina-finai ne tun lokacin da take da aure.
A cewarta, "Karance-karancen littafai da kallon fina-finan tarihi ne suka sa na soma sha'awar shiga fim.
"Na kalli fim din 'Ki Yarda Da Ni' a lokacin ina gidan mijina, kuma da aurena ya zo karshe sai na ji sha'awar shiga fim. Na soma fim ne sama da shekara 16 da suka wuce kuma na fito a fim fiye da 300.''
"Wani darakta ne marigayi Tijjani Ibrahim ya tambaye ni irin rawar da na fi so na taka a fim, ni kuma na ce masa na fi son fitowa a matsayin uwa.
"Shi ya sa tun daga wancan lokaci nake fitowa a matsayin uwa, tun ma ina da kuriciya ake yi min kwalliya irin ta uwa domin na taka irin wannan rawar."
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Kannywood Sunzama Dankali Sha Kushe-Hadizan Saima
Description : Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun za...
Rating :
5