Ministan shari'ar Najeriya, Barista Abubakar Malami ya ce tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fensho garambawul, ya bukaci samun damar koma wa Najeriya don ya taimaka wajen dakile wata gagarumar almundahana da ke gudana.
Ya ce Abdulrashid Maina ya fada masa yayin ganawarsu a Dubai cewa akwai wani rukunin masu cin hanci da ke wawure naira biliyan biyar duk wata daga kudaden gwamnati na biyan fensho.
A cewarsa: "wanda (Maina) ke cewa kuma gaskiyar al'amari abin da ake bukata domin biyan fensho bai wuce biliyan daya da miliyan 300 ba".
Abubakar Malami ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da BBC yayin wata ziyara da ya kawo a baya-bayan nan zuwa ofishinmu na London.
Badakalar tsohon babban jami'in fenshon da ake nema ruwa a jallo da kuma mayar da shi bakin aiki a gwamnatin Buhari ta janyo zazzafar muhawara da suka a tsakanin 'yan kasa.
An dai rika nuna dan yatsa ga ministan shari'ar Abubakar Malami da takwaransa na harkokin cikin gida Abdurrahman Bello Dambazau da kuma shugabar ma'aikata Misis Winifred Oyo-Ita game da wannan abin kunya.
Ministan shari'ar ya ce sun yi ganawar ce a watan Janairun shekara ta 2016, amma ya musanta amincewa da bukatar Maina.
"Maina ya rubuto wasika ta hanyar lauyansa yana rokon cewa ofishin atoni janar (ofishina) ya duba ya ba da shawara kan a mayar da shi aiki.
Sanadin wannan bukata ga tsari na al'adar aiki na tura takardar bukatarsa zuwa ga wani cikin ma'aikata cewa a duba a shawarci ministan shari'ah a kai. Kuma aka dawo da shawara wadda ministan ya dauki mataki na cewa a sake duba ta saboda an ambaci wasu shari'o'i...", in ji Malami.
A cewarsa bayan wannan ganawa, sun dauki matakin bincike kan wannan badakala, inda suka bankado gungun wasu jami'ai da ke kulle-kullen satar irin wadannan kudade.
Da aka tambaye ko me ya sa suka yi wannan al'amari a rufe duk da yake hukumar EFCC tana neman Abdurrashid Maina ruwa a jallo, Abubakar Malami ya ce ba haka batun yake ba.
Ya ce: "Gaskiyar al'amari daga cikin takardun da lauyan Maina ya gabatar wa gwamnati akwai wadda ta nuna cewa tun a shekara 2013 zuwa 2014, tsohon jami'in fenshon ya shigar da kararraki ciki har da wadda ta bukaci a cire sunansa daga jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo."
Barista Malami ya ce kuma har Maina ya samu nasara a kotun tun kafin zuwan gwamnatinsu, kuma tun a wannan lokaci kuma yana da damar shigowa Najeriya.
Ya musanta yin wata rufa-rufa wajen mayar da Abdulrashid Maina kan aiki.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC dai na neman Abdurrashid Maina ruwa a jallo.
Source: BBC Hausa
Title :
Wasu Na Wawure Naira Biliyan 5 Duk Wata A Nijeriya
Description : Ministan shari'ar Najeriya, Barista Abubakar Malami ya ce tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fensho garambawul, ya bukaci samun damar...
Rating :
5