Abubuwa da dama sun faru a shekarar 2017, ciki har da muabus din Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da kuma wani sauyi makamancinsa da aka samu a Gambiya da Angola.
Ba kuma za a manta da soke zaben shugaban kasa da kotu ta yi ba a Kenya, wanda shi ne karo na farko da aka taba samun irin haka a Afirka.
Mun kuma kawo muku rahotanni a kan labaran tashin hankali da na kirkire-kirkire - amma a nan wasu sabbin labarai ne da watakila ba ku ji su ba a cikin shekarar 2017.
'Dan ta-kifen da kafafen sada zumunta suka sa ya yi zarra a Kenya'
Wani dan Kenya yana cin githeri, wani nau'in abinci ne da ake ci sosai a kasar, wanda ake dafa masara da wake, yana da cika ciki, yana da gina jiki da kuma araha, a watan Agusta lokacin da ake zabe, mutumin ya yi suna sosai kawai saboda yadda ya dinga cin githeri a kan layin za.
An yi ta tattauna batun mutumin wanda aka sanyawa sabon suna 'Mai cin Githeri' a kafafen sada zumunta na zamani
'Yan kasar Kenya da dama sun kaunaci Martin Kamotho, saboda yanayin tsayuwarsa, da rigar da ya sa, da yadda ya dinga cika bakinsa da githeri, da kuma rike ledar da ya yi mai dauke da abincin, duk cikin saukin kai.
Yanayinsa ya wakilci abubuwa da yawa ga mutane daban-daban, amma mafi yawa sun dauke shi a matsayin wani tsageri, ko 'dan-ta-kife', ko dan ba-ruwana, ko kuma mai saukin kai.
A sakamakon haka a yanzu dai Mista Kamotho ya yi fice sosai da sunan 'Mai cin Githeri' kuma ya zama wani da ake yada shi sosai a shafukan sada zumunta a matsayin mai barkwanci:ce da ya yi ya sa an yi ta hira da shi a wasu tasoshin talabijin na kasar.
Ficen da yake kara yi a kullum, ya sa kamfanoni da dama a Kenya suke ganin ya zama wata hanyar samun kudi da za su yi mu'amala da shi.
A sakamakon farin jinin da ya yi dai ya samu kyautar fili, an kuma dauki nauyin kai shi yawon bude ido wani shahararren gandun daji na Maasai a Kenya, da kuma kyautar wayoyin komai da ruwanka da aka ba shi shi da iyalansa.
Kuma Mista Kimontho ya kasance daga cikin 'yan kasar 59 da suka sami jinjina daga shugaban kasa kan aikin da ya yi wa kasar a lokacin bukukuwan tunawa da ranar samun 'yanci na Kenya.
A cewar jaridar Daily Nation, an bayar da lambar yabon ne don girmama mutanen da suka nuna "wasu dabi'u da za a iya koyi da su, ko cimma wasu nasarori na gwarzantaka ko kishin kasa ko kuma shugabanci."
Wasu 'yan kasar har yanzu suna mamakin wanne abu Mista Kimotho ya yi da har ya cancanci irin wannan lambar yabo da jinjina.
Jami'in FRSC a Najeriya ya 'ci mutuncin mata'
A watan Afrilu, Hukumar Kiyaye Kare Afkuwar Hadurra ta Najeriya ta ladabtar da wani babban jami'inta bayan da aka dauki bidiyonsa yana horar da wasu jami'an hukumar mata hanyar yanke musu dogon kashin kansu.
Hotuna sun nuna yadda jami'in ya dauki almakashi ya dora a kan gashin matan, a yayin da suke wani fareti, al'amarin da ya janyo matukar ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta na kasar.
A bisa doka dai matan sun kaucewa ka'idar aikin hukumar ne na yadda mata za su gyara gashin kansu.
Wata mataimakiya ga Shugaba Muhammadu Buhari ta yi Allah-wadai da abun da jami'in ya yi, tana mai cewa 'hakan cin zarafin mata ne
Wani mai magana da yawun hukumar FRSC ya ce halayyar da babban jami'in ya nuna ta kaucewa ta hukumar.
Wata mataimakiya ga Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ta yi Allah-wadai da abun da jami'in ya yi a shafinta na Twitter, tana mai cewa 'hakan cin zarafin mata ne.'
'Cocin
Wata hudubar da aka sabaugabannin cocin darikar evangelical ga mabiyansu ita ce, su guji mu'amala da masu shan barasa da sigari.
Amma wani sabon coci a Afirka Ta Kudu yanantar wannan huduba, inda yake nuna cewa a yi mu'amala da masu shan barasa da sigari maimakon kaurace musu.
Cocin Gobola da ke birnin Johannesburg ya bude kofofinsa da kwalabansa ga masu tu'ammali da barasa, inda yake raba musu barasa a lokacin da ake addu'i'i, a cewar kafar yada labarai ta Afirka Ta Kudu ta eNCA.
Faston cocin Tsietsi Matiki ya ce, cocin waje ne da ya dace sosai da mashaya barasa da masu shan sigari.
Sai dai hukumar kula da coci-coci ta kasar ta ki amincewa da cocin, in ji eNCA.
Wani mabiyin cocin Gobola ya ce, a kan bayar da barasar ce ga wadanda suka kai shekara 20, wato wadanda suka wuce shekarun da dokar kasar ta yi umarnin shan barasa da shekara biyu.
Masu sanko na cikin barazana
A watan Yuni ne, 'yan sanda a Mozambique suka gargadi masu sanko da yi taka tsan-tsan bayan samun rahotanni cewa matsafa na hakonsu don kashe su.
Kwamandan 'yan sanda na tankin Zambezi da ke tsakiyar Mozambique ya yi gargadi cewa hare-haren suna da alaka da imanin da wasu suka yi cewa ana samun zinare a kawunan masu sanko.
A kalla mutum uku aka kashe a yayin da muka hada wannan labari.
'Yan sanda sun kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da kashe mutane don yin tsafi.
'Yan majalisa sun bai wa hammata iska a Uganda
Wani kokari da 'yan majalisar jam'iyya mai mulki a Uganda suka yi na yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don cire yawan shekarun tsayawa takarar shugaban kasa ya jawo an bai wa hammata iska a majalisar.
'Yan majalisa daga jam'iyyar adawa sun ce yin hakan wata makarkashiya ce ta gyarawa Shugaba Yoweri Museveni mai shekara 73, hanya don yin takarar shugabancin kasar a zaben 2021.
A karkashin tsarin mulkin da kasar ke amfani da shi yanzu dai, ba a so duk wanda ke son tsayawa takarar shugaban kasa ya wuce shekara 75.
An yi ta jifa da kujeru a yayin muhawarar a majalisar dokokin
A bangare guda kuwa, 'yan majalisar dokokin Afirka Ta Kudu sun yi abun da ya fi na 'yan majalisar dokokin Uganda kamari.
'Yan majalisar jam'iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters, sun yi arangama da jami'an tsaro a watan Fabrairu, sakamakon kin bin umarnin da aka ba su na daina katse Shugaba Jacob Zuma a yayin da yake jawabi ga 'yan kasar.
Fada ya kaure sosai a yayin da jami'an tsaro suka yi kokarin fitar da 'yan majalisar daga zauren.
A karshe dai sun yi nasarar fitar da 'yan majalisar amma fa an sha artabu:
Tsallake Youtube wallafa daga ODN
Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne
Karshen Youtube wallafa daga ODN
An haramta sa wando a Sudan
'Yan sanda a Sudan sun kai samame wajen da aka yi wata liyafa a babban birnin kasar Khartoum, a watan Disamba inda suka samu wasu mata sanye da wanduna.
An kama matan 24 aka kuma tuhume su da rashin kamun kai, amma daga bisani aka dakatar da tuhumar.
'Yan sandan da ke kula da bangaren da ke tabbatar da cewa da'a ne suka kai samamen.
Idan da a ce an gurfanar da matan, da za su iya fuskantar hukuncin bulala 40 da kuma tara, saboda sanya kayan 'da ba su dace ba.'
Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce an sha kama dubban mata tare da yi musu bulala ko wacce shekara, kuma sun ce za a iya sanya doka ba tare da tsawwala ba.
Sun kara da cewa wannan dokar a kasar da Musulmai suka fi yawa ta hana sanya dogon wando ko gajere ko kuma matsattsen siket, tamkar nuna wariya ce ga Kiristoci.
A al'adance dai mata a Sudan kan sanya dogayen riguna ne.
Wata mai fafutuka Amira Osman ta shaidawa wani gidan rediyon kasar Netherlands, Dabanga, cewa wannan doka ta take hakkin mata.
Ta ce: "An yi liyafar ne a wani rufaffen waje da ke cikin wani gini na El Mamoura a kudancin birnin Khartoum."
"An kama 'yan matan saboda sun sanya wando, duk da cewa sun samu izinin yin liyafar daga hukumomi," in ji Amira.
#WengerOut
An ci gaba da samun rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kan kocinta Arsene Wenger, a nahiyar Afirka da ma wasu wuraren.
A watan Nuwamba dai, a yayin da mafi yawan 'yan Zimbabwe suke murnar kwace mulki da sojoji suka yi daga hannun Robert Mugabe har suka bazu kan tituna suna bukatarsa da ya yi murabus, a sannan ne wasu magoya bayan Arsenal su ma suka bazama tituna suna kiran Wenger da ya yi murabus.
Amma dai hakan ya zama tamkar wani take da aka yi yayi a shekarar nan. An yi irin hakan ma a yayin da ake wani wasa a Habasha a ranar 16 ga watan Afrilu, kwanaki kadan bayan da Crystal Palace ta ci Arsenal a wata fafatawa da suka yi:
Hatsari biyu, ganau daya
Wani dan kasar Kenya ya yi wani abu da ya kullewa mutane na tsawon kwanaki bayan da ya bayar da labarin wasu munanan hadurra biyu da suka faru a kan idonsa, a wasu sassan kasar biyu daban-daban.
An yi ta yada wasu hotuna da wani gidan talbijin ya nuna na mutumin a lokacin afkuwar hadurran, a shafukan sada zumunta.
Mutumin mai suna Dennis Muigai ya yi hira da gidan talbijin na Citizen bayan wani mummunan hatsarin helikwafta da aka yi ranar 21 ga watan Oktoba, inda a kalla mutum biyar suka mutu.
Ya kuma sake shaidar wani hatsarin a ranar 7 ga watan Nuwamba a yankin Murang'a, da ke tsakiyar Kenya, mai nisan kilomita 200 daga inda hatsarin farkon ya faru, inda har wani gwamna ya mutu.
Ya kuma sake shaida wa wani gidan talbijin na NTV cewa, yana cikin fasinjoji ne a wata motar 'yan sanda a lokacin afkuwar hatsarin, ya kuma yi bayanin abun da ya gani.
A cewar kafar yada labarai ta Nairobi News, ya ce abun da ya fara yi bayan afkuwar hatsarin shi ne ya zare bindigar mai tsaron gwamnan da kuma kayayyakin mutanen cikin motar.
Sai dai wata kafar yada labarai ta kasar ta ruwaito cewa daga baya ne 'yan sanda suka kama Mista Muigai saboda yin badda kama a matsayin dan sanda. Ba a dai kara sanin me ya faru da shi ba tun lokacin.
A duk hirar da aka yi da shi a gidajen talbijin din, ya manna bakin tabarau a idonsa wanda ke hade da wata na''urar sauraron sauti ta kunne, wanda hakan ya jawo aka yi ta tattauna yanayin shigar tasa a shafukan sada zumunta har ake zolayarsa, aka kuma kirkiri wani maudu'i mai taken #WitnessChallenge a shafin Twitter, inda har wasu suka yi ta kwaikwayon shigar tasa:
Source: BBC Hausa