Liverpool za ta kara da Everton, yayin da masu rike da kofi Arsenal za su fafata a gidan Nottingham Forest a wasannin zagaye na uku na gasar cin kofin FA.
Jagorar gasar Premier Manchester City za ta kara a gida da Burnley, yayin da Manchester United za ta karbi bakuncin Derby, sanna kuma Chelsea za ta je gidan Norwich.
Slough Town, wadda ita ce kungiya mafi kankanta a jadawalin da aka fitar za ta je gidan Doncaster idan har ta doke Rochdale ranar Litinin.
Wata karamar kungiyar Hereford za ta kara da Leicester, idan ta yi nasara a kan takwararta ta Fleetwood a wasan da za su sake.
Kungiyar AFC Fylde za ta je gidan kungiyar Premier ta Bournemouth idan har ta yi nasarar doke Wigan a wasan raba gardama. Woking, wadda ita ma karamar kungiya ce a gasar rukuni na biyar a Ingila, idan ta dace da nasara a kan Peterborough su ma a wasansu na biyu za su cancanci zuwa gidan Aston Villa.
A sauran wasannin AFC Wimbledon za ta je filin wasa na Wembley ta fafata da Tottenham, ita kuwa Middlesbrough za ta hadu da Sunderland yayin da Brighton & Hove Albion za ta karbi bakuncin Crystal Palace.
Za a yi wasannin ne a karshen makon 6-7 na watan Janairu na shekara mai kamawa ta 2018.
Source: BBC Hausa
Title :
Wasannin Da Zaa Buga A Kofin FA
Description : Liverpool za ta kara da Everton, yayin da masu rike da kofi Arsenal za su fafata a gidan Nottingham Forest a wasannin zagaye na uku na gasar...
Rating :
5