Yan sanda a birnin Hyderabad na kasar India sun ce sun kama wani mutum bayan ya kona wata mata sakamakon sabanin da suka samu.
Sandhya Rani, mai shekara 25, tana kan hanyarta ta komawa gida daga inda take aiki lokacin da mutumin ya kai mata hari ranar Alhamis da rana, in ji 'yan sanda a hirarsu da BBC.
Mutane sun ruga da ita asibit amma kafin su je ta mutu.
Mutumin da ake zargi da kisa, Karthik Vanga, mai shekara 28, tsohon abokin aikinta ne.
'Yan sanda sun ce Vanga ya je wurin Ms Rani ranar Alhamis inda aka gan su suna takaddama, sai kawai ya fito da jarkar fetur ya watsa mata a jiki kana ya cinna mata wuta.
Sun kara da cewa ana zargin mutumin ya dauki matakin ne saboda ta ki amincewa ta aure shi bayan ya kashe shekara biyu yana nemanta.
Cin zarafin na karuwa sosai a India tun daga shekarar 2012 lokacin da wani gungun mutane ya yi wa wata dabila fyade da ke cikin tasi tare da su a Delhi, babban birnin kasar.
Source:BBC Hausa
Title :
Wani Yakashe Matan Dataki Aurensa a Indiya
Description : Yan sanda a birnin Hyderabad na kasar India sun ce sun kama wani mutum bayan ya kona wata mata sakamakon sabanin da suka samu. Sandhya Rani...
Rating :
5