Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar wuni biyu a Kano daga ranar Laraba zuwa Alhamis, inda ya samu tarba daga gwamnati da al'ummar jihar.
Wannan shi ne karon farko da shugaban ke yin wannan ziyarar tun bayan ya zaman shugaban kasa sama da shekara biyu da suka wuce.
Kano ita ce cibiyar siyasar shugaban kasar sai dai wasu mazauna jihar na ganin bai kyauta musu ba saboda rashin ziyararsu da ma gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya.
Sai dai wasu magoya bayansa sun ce suna tare da shi komai ruwa komai dari saboda, a ganinsu ya tabbatar da tsaro a jihar da ma arewacin Najeriya, lamarin da ya dade yana ci musu tuwo a kwarya.
Yanzu dai tambayar da ke bakin mutane ita ce, shin wane tasiri ko sauyi za a samu bayan ziyarar shugaban na Najeriya a cibiyarsa ta siyasa?
Shin masu guna-guni da rashin zuwa Buhari Kano a yanzu za su daina?
An jima 'yan hamayya da ma wasu magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari suna korafi kan rashin ziyararsa Kano.
A zaben 2015 Buhari ya samu kuri'a miliyan 1.9, abin da ya taimaka masa wajen kayar da shugaba mai ci Goodluck Jonathan.
Mutane da dama sun yi zaton cewa shugaban zai kai ziyarar godiya ga Kanawa cikin dan kankanen lokaci da fara mulkinsa.
Hakan ce ta sa da aka shafe sama da shekara biyu mutane ke korafin Buhari ya yi wa Kano butulci, ko da yake kakakin shugaban kasar Mallam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa 'ko kadan Shugaba Buhari ba shi da niyyar mayar da Kanawa saniyar ware.'
"Yanzu magoya bayan Shugaba Buharin sun samu bakin magana, sannan an rufe bakin masu korafin cewa ya manta da su," in ji shi.
Yadda Kanawa suka zabi Buhari
Irin kuri'un da suka kada masa a 2015
9,401,288
Yawan al'ummar Kano
2,172,447 Yawan kuri'un da aka kada a zaben 2015
1,903,999 Kuri'un da Buhari ya samu
215,779 Kuri'un da Jonathan ya samu
INEC da Hukumar Kidayar Jama'a ta Najeriya
Ofishin Shugaban Najeriya
Samar da ayyukan gwamnatin tarayya
Wani tasiri da ake fatan ziyarar Shugaban za ta yi ita ce wajen samar da ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.
Kawo yanzu babu wasu ayyuka na a zo a gani da gwamnatin Buhari ta yi a Kano kamar yadda ta fara a wasu wuraren tun bayan hawansa mulki.
Malam Kabiru Sufi da ke sharhi kan al'amuran siyasa ya ce mai yiwuwa ziyarar ta haifar da sauye-sauye.
"Mai yiwuwa a ganawar da Shugaba Buhari zai yi da jama'ar Kano a rana ta biyu ta ziyarar, jama'a za su samu damar mika korafe-korafensu ga Shugaban Buhari, ciki har da bukatar kawo manyan ayyuka jihar.
"Kuma idan shugaban ya amsa to za a iya cewa kwalliya ta biyan sabulu", in ji shi.
Soyayyar Kanawa ga Buhari
Tun lokacin da Muhammadu Buhari ya shiga siyasa a 2002 mutan Kano su ke nuna masa zazzafar kauna da fatan cewa idan ya samu mulki za su kasance cikin wadanda za su ci moriyar gwamnatinsa.
Muhimman abubuwan da Kanawan ke sa ran gwamnatin Buhari za ta yi musu tun daga 2015 sun hada da gyara hanyar Kaduna zuwa Kano, wacce ta yi mummunar lalacewa take kuma janyo asarar rayuka da dukokiyoy a kullum.
Kazalika jama'ar Kano da dama na fatan ganin gwamnatin Buhari ta gaggauta gudanar da manyan ayyuka kamar aikin fadada hanyar jiragen kasa, da kammala fadada hanyar Kano zuwa Maiduguri.
'Yan siyasa da dama na ganin Shugaban bai saka musu ba ta wajen ba da mukamai ga mutanen da suka jima suna wahalta masa a siyasance. Ko da dai Buhari ya bai wa mutane da dama mukamai, amma wasu na ganin har yanzu jihar na bin Buhari bashi.
Sasanta rikicin APC a Kano: Tun bayan zaben 2015 dangantaka ta yi tsami tsakanin yayan jam'iyyar, inda ake da shugabanci biyu. Wasu na ganin sakacin Buhari wajen rashin sasanta rikicin, kuma suna fatan ganin ya daidaita bangarorin.
Farfado da farin jinin Shugaba Buhari
Wani tasirin da ake gani ziyarar za ta yi shi ne farfado da farin jinin Shugaba Buhari a wajen wasu da suka fara dawowa daga rakiyarsa.
Ziyarar, a cewar masu irin wannan ra'ayi ta wankewa mutane da dama takaicin da suka jima suna yi na rashin zuwan Buhari Kano.
Kuma mai yiwuwa hakan ya yi tasiri a zaben shekarar 2019, da alamu ke nuna Shugaban zai sake tsayawa takara.
A lokacin ziyarar dai, Shugaba Buhari zai kai ziyara wasu masana'antu na masu zaman kansu.
A cewar Malam Kabiru Sufi, hakan wata alama ce ta nuna gamsuwar gwamnati da masu masana'antu da kara musu karfin gwiwa.
Gyara gidan kurkuku na Kurmawa
Wani alfanun da magoya bayan Shugaba Buhari ke cewa za a samu, shi ne gyaran gidan kurkuku na Kurmawa, inda tun da farko shugaban ya ziyarta, har ma ya shaida sakin fursunoni 500 da gwamnatin Kano ta dauki nauyin biya musu tara.
Mai taimakawa shugaban kan harkokin rediyo da talabijin Sha'aban Ibrahim Sharada, ya ce: "Shugaban ya yi alkawarin gyara gidan yari na Kurmawa wanda aka gina shekara 100 da suka gabata".
Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGESImage captionMutane sun yi ta murna a lokacin da aka sanar da lashe zaben Buhari a 2015
Babu karsashi
To sai dai wasu na cewa ziyarar ba ta yi armashi ba, kasancewar a ranar farko ta ziyarar Shugaba Buhari ba shi da karsashin da ya saba nunawa a lokutan da yake kai ziyara a baya.
Hatta jawabin da ya gabatar a wajen bude daya daga asibitoci biyu da gwamnatin Kano ta gina, ya yi shi ne takaitacce, kuma babu wani albishir da ya yi wa Kanawa a lokacin jawabin.
Gaza sasanta rikicin siyasa
Haka kuma wasu masana na ganin ba a yi amfani da ziyarar yadda ya kamata ba, musamman wajen sasanta rikicin siyasa tsakanin 'yan jam'iyyar APC a jihar.
Malam Kabiru Sa'idu Sufi ya ce: "Da Buhari ya yi amfani da ziyarar wajen sasanta rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso da Ganduje da hakan ya kara wa jam'iyyar karfi, sannan da hakan ya zama abin misali ga sauran jihohin da ke da irin wannan matsala.
Source: BBC Hausa