Hukumar kwallon kafa ta Wales ta kawar da yuwuwar daukar dan Ingila a matsayin kocin tawagar yankin na gaba.
Hukumar na fatan ganin ta samu wanda zai gaji Chris Coleman a kan lokaci domin tunkarar gasar kasashen Turai ta Natios League ranar 24 ga watan Janairu.
Shugaban hukumar kwallon ta Wales Jonathan Ford ya ce a ko da yaushe sukan dauki 'yan Wales a wannan aiki, saboda suna da sha'awar aikin, to amma a wannan karon dan waje za su dauka amma kuam ba dan Ingila ba.
Kociyoyin Wales shida na baya bayan nan ciki har da na rikon kwarya dukkaninsu 'yan yankin ne, in banda Bobby Gould, dan Ingila wanda ya rike tawagar daga 1995-1999.
Kociyan na baya bayan nan Chris Coleman ya raba gari da Wales din saboda kasa samun gurbin gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai kamawa ta 2018 a Rasha, a bazara mai zuwa.
Yayin da yankin ke ci gaba da neman kociya, Wales din ba ta da wani wasa a nan gaba, sai a gasar China Cup a shekara ta 2018 mai kamawa.
Source: BBC Hausa
Title :
Wales Bazasu Dauki Koci Dan Ingila Ba
Description : Hukumar kwallon kafa ta Wales ta kawar da yuwuwar daukar dan Ingila a matsayin kocin tawagar yankin na gaba. Hukumar na fatan ganin ta samu...
Rating :
5