Lokacin kirsimeti da sabuwar shekara lokaci ne da mabiya addinin kirista ke yin tafiye-tafiye, wanda wasu shugabannin addinin kirista suka ce tafiye-tafiyen na da asali a ekilisiyya.
Wasu mabiya na kokarin sada zumunci a wannan lokaci, amma wasu na ganin a yadda al'amuran rayuwa suke tafiya, tafiye-tafiye ba su zama dole ba.
A daidai wannan lokaci na kirsimeti da sabuwar shekara mabiya addinin kirista kan bar wuraren da suke domin komawa mafari, wato garuruwansu na asali, akasari domin sada zumunta.
Reverend John Joseph Hyab, wani malamin addinin kirista a Najeriya ya ce tafiye-tafiyen mabiya addinin kirista na da asali ne a ekilisiyya.
"Duk wanda ya san littafi mai tsarki wato labarin haihuwar Yesu to ya san cewa haihuwar Yesun ta hada da tafiye-tafiye, tun lokacin da Mala'ika ya bayyana gaban Maryamu ya ba ta busharar za ta haihu a lokacin ya kuma shaida mata cewa Elizabeth mahaifiyar Yohanna na da juna biyu, to sai Maryamu ta ziyarce ta don taya ta murna," in ji Reverend Hyab.
Sai dai mabiya addinin suna korafin cewa a wannan lokaci da yawa ba su da halin yin tafiye-tafiyen saboda halin matsin rayuwar da ake ciki.
Mista Adamu Marshall ya ce wani lokaci dole ne wasu sai sun yi kaura daga birane zuwa garuruwan da aka haife su.
"Eh tafiya na da amfani don akwai wadanda ke zaune a birane kuma iyayensu na kauye, kuma wannan ne kawai lokacin da akan samu damar zuwa a gaida iyaye. Shi ya sa ake amfani da damar don yin ziyara.
"Kuma tafiya ta yi wahala ne a wannan zamanin saboda tsadar rayuwa wanda ina ganin laifin gwamnati ne, ai a wasu kasashe a irin wannan lokacin komai sauki yake kara yi ba wahala ba, amma a Najeriya komai kara tsawwala yake," in ji Adamu Marshal.
Yayin da Adamu Marshall ke nuna alfanun irin wannan bulaguro, shi Mista Modekai Ibrahim na ganin in dai ba da wani uzuri ba, shi ya gwammace ya yi zamansa a inda yake.
"Yanzu idan na ce zan je gida sai na sha mai rabin tanki, to ka ga da wannan kuwa ai gara na saya wa iyalina kaji su ci.
"Masu sayar da mai da gangan suke bullo da wanann wahalar, tun da sun san cewa a wannan lokaci na kirsimeti ana yawan yin tafiye-tafiye. Haka ba kyau gaskiya., in ji Mista Marshall.
Da yawan Jama'ar Igbo daga kudu maso gabashin Najeriya da ke zaune a arewa, kan bar arewa don komawa yankinsu tun kafin Kirsimeti, wasun su kuma su zauna a gida har sabuwar shekara.
Chief Dominic Uzu ya ce nauyin sarauta ne ke sanya shi tafiya gida, ba don haka ba lokacin sabuwar shekara da kirsimeti ba lokaci ne na tafiye-tafiye a halin da ke kasar ke ciki yanzu.
Hausawa dai kan ce zumunci a kafa yake ,kuma kowa ya bar gida gida ya bar shi kila laakari da haka ne kan sa mabiya addinin kirista lekawa gida a lokacin kirsimeti da sabuwar shekara .
Source: BBC Hausa
Title :
Wahalar Rayuwa Ta Hana Kiristoci Ziyara Lokacin Kirismeti
Description : Lokacin kirsimeti da sabuwar shekara lokaci ne da mabiya addinin kirista ke yin tafiye-tafiye, wanda wasu shugabannin addinin kirista suka c...
Rating :
5