Gwamnatocin Turai suna da hannu a cin zarafin 'yan cirani da 'yan gudun hijira a Libiya, in ji kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International .
Kungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wani rahoto inda ta kara da cewa a kokarinta na dakile kwararar bakin haure, kungiyar tarayyar Turai tana taimaka wa "wani shirin cin zarafin" bakaken fata a gabar tekun Libiya.
Kudaden kungiyar tarayyar Turai suna zuwa ga hukumomin da ke aiki da mayaka da kuma masu safarar mutane, in ji rahoton.
Kungiyar tarayyar Turai ta bayar da jiragen ruwa da horaswa da kuma kudi ga jami'an tsaron gabar tekun Libiya.
Libiya ita ce hanyar da 'yan ci-rani masu son zuwa Turai suka fi bi wurin isa Italiya.
Amma Amnesty ta ce jam'ian tsaron suna aiki da 'yan daba masu laifi da kuma masu safarar mutane wadanda aka samu da laifin nau'o'i na cin zarafi, da sanin jami'an kungiyar tarayyar Turai.
Kungiyar Amnesty ta yi zargin cewa kokarin dakile kwarar bakin haure ya janyo "kama mutane da yawa da kuma daure su ba gaira ba dalili".
Source: BBC Hausa
Title :
Turai Nada Hanu A Cin Zarafin Yan Ci Rani A Libya
Description : Gwamnatocin Turai suna da hannu a cin zarafin 'yan cirani da 'yan gudun hijira a Libiya, in ji kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amn...
Rating :
5