Kasar Tunisiya ta sanar da haramta saukar duk wani jirgin sama a kasar daya fito daga Hadaddiyar Daular Larabawa saboda dalilan tsaro.
Sanarwar na zuwa ne kwana biyu bayan jami'an gwamnatin Tunisiya sun yi zargin cewa Hadaddiyar Daular Larabawar ta haramtawa matan Tunisiya tafiye-tafiye ta jirgin sama zuwa kasar ko kuma yada zango a cikin kasar ta.
Wasu matan Tunisiyar da suka yi balaguro zuwa kasar sun yi korafin cewa, an jinkirta tafiyarsu a jirgin Emirates, inda wasun su suka ce sai da aka sake tantance takardunsu na Visa.
Ma'aikatar kula da harkokin sufuri a Tunisiyar ta ce haramcin saukar jiragen saman zai ci gaba har sai an dauki matakan da suka kamata.
Kawo yanzu dai ba bu wani martani daga Hadaddiyar Daular Larabawar.
Source: BBC Hausa
Title :
Tunusiya Tahana Jiragen Emirate Sauka A Kasar Sabida Tsaro
Description : Kasar Tunisiya ta sanar da haramta saukar duk wani jirgin sama a kasar daya fito daga Hadaddiyar Daular Larabawa saboda dalilan tsaro. Sana...
Rating :
5