Al'umar kasar Liberia na ci gaba da murna da shagali tun bayan sanar da sunan tsohon shahararren dan kwallon kafa George Weah a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka je zagaye na biyu.
Bayan da aka kidaya kuri'u daga kusan dukkan mazabun kasar, kuma bayan zaben da aka yi a zagaye na biyu, George Weah ya tserewa abokin karawarsa, Joseph Boakai nesa ba kusa ba.
Zai gaji Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da aka taba zaba a matsayin shugabar kasa a Afirka, kuma a zaben demokradiyya na farko da zababbe zai mika wa wani zababben tun bayan yakin basasar kasar.
Mrs Sirleaf ta doke Mista Weah a zaben shugaba kasar da aka gudanar, shi ma a zagaye na biyu, a 2005 bayan yakin basasar kasar.
Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.
Yakin neman zaben Mista Weah a karkashin hadakar jam'iyyun siyasa ta CDC - Coalition for Democratic Change - ya burge matasa sosai, amma abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Mista Boakai bai sami karbuwa sosai ba.
Kuma matar tsohon shugaba Charles Taylor, Jewel Taylor ce mataimakiyarsa, duk da cewa shi Charles Taylor din na tsare a wani gidan yari dake Burtaniya a sanadiyyar samunsa da laifukan yaki da aka yi a makwabciyar kasar Saliyo.
A watan Oktoba, Mista Weah ya lashe zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar, inda ya sami kashi 38.4 cikin dari, shi kuwa mai binsa a baya, Mista Boakai dan shekara 73 ya samu kashi 28.8 cikin dari.
Rashin samun wanda yayi nasara kai tsaye ne ya janyo aka gudanar da zaben a zagaye na biyu.
Hukumar zaben kasar ta Laberiya ta ce an kammala kidayar kashi 98.1 cikin dari na kuri'un da aka kada, kuma zuwa ranar yau Alhamis, Mista Weah ya lashe kashi 65.5 cikin dari na kuri'un.
Mista Boakai kuma na da kashi 38.5 cikin dari ne na dukkan kuri'un.
Mista Weah ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa kamar AC Milan da Chelsea da Paris St-Germain, kuma shi ne dan Afirka tilo da ya taba lashe lambar dan wasa mafi shahara a duniya da kungiyar FiFA ke bayarwa da kuma lambar Ballon D'Or.
Ya shiga siyasa bayan da ya daina buga wasan kwallo a 2002, kuma a halin yanzu yana rike da mukamin sanata ne a majalisar Laberiyan.
Kararraki da aka shigar a kotu ne suka hana a gudanar da zaben a watannin baya, kuma masu kada kuri'a basu fito sosai ba.
Jami'an zabe sun ce kashi 56 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a ne suka fita zuwa rumfunan zabe.
Fiye da mutum miliyan biyu ne suka yi rajista a kasar ta Laberiya mai mutane kimanin miliyan 4.6.
Mrs Sirleaf ta zama shugabar kasa a 2006 bayan da 'yan tawaye suka fatattaki Charles Taylor a 2003, dalilin da ya kawo karshen yakin basasar kasar.
A halin yanzu Charles Taylor na zaman kaso na tsawon shekara 50 a Burtaniya saboda laifukan yaki dangane da yakin kasar Saliyo.
Source: BBC Hausa
Title :
Tsohon Danwasa Yazamo Shugaban Kasan Liberiya
Description : Al'umar kasar Liberia na ci gaba da murna da shagali tun bayan sanar da sunan tsohon shahararren dan kwallon kafa George Weah a matsayin...
Rating :
5