An dage biyu daga cikin wasannin ranar Talata na zagaye na biyu na gasar cin kofin FA da kuma gasara tseren doki ta Ayr saboda tsananin sanyi.
Sanadiyyar kankara a filayen wasan ne aka dage karawar ta gasar ta FA tsakanin Crewe da Blackburn Rovers da kuma ta Carlisle da Gillingham.
Yayin da aka dage wasan na Crewe zuwa ranar Laraba 13 ga watan nan na Disamba da karfe 7:45 agogon GMT, ba a tsayar da ranar da za a yi daya wasan ba.
Haka ita ma gasar tseren dokin ta Ayr an dage ta ne saboda filin tseren ya daskare da kankara.
Source: BBC Hausa
Title :
Tsananin Sanyi Yasa Andage Wasan FA A Ingila
Description : An dage biyu daga cikin wasannin ranar Talata na zagaye na biyu na gasar cin kofin FA da kuma gasara tseren doki ta Ayr saboda tsananin sany...
Rating :
5