Shugaban Amurka Donald Trump ya jinjina wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri.
A wani sako da ya rubuta a shafinsa na twitter, Mr Trump ya ce hakan ya jaddada cewa duniya na bukatar zaman lafiya ne ba kashe-kashe ba.
A cewar Amurka, Koriya ta Arewa ta shigar da gangar tattacen man fetur miliyan 4 da rabi a shekarar 2016.
Sai dai a yanzu wannan kudiri da a ka dauka zai kayyade ma Koriya ta Arewa ikon shigo da man fetur din zuwa ganga dubu 500 a shekara guda.
Hakan zai zaftare kusan kashi 90 a kudirin Kim Jong-un na son zama Shugaban kasar na har abada.
Fitar da man fetur din Pyongyang zai ragu da kusa kashi 90 cikin dari kuma za a bukaci 'yan Koriya ta arewar da ke aiki a wasu kasashen duniya da su dawo gida.
Kuma hakan zai dakile wata muhimmiyar kafa ta samun kudaden kasashen waje.
Source: BBC Hausa
Title :
Trump Ya Yabi MDD Kan Takunkumin Koriya Ta Arewa
Description : Shugaban Amurka Donald Trump ya jinjina wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri. A...
Rating :
5