Matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan ayyana Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila ya jawo wa Amurka abin da ya fi suka daga wajen kawayenta.
A wani taron tsaro na shekara-shekara na Manama da ake gudanarwa a Bahrain, kusan gaba dayan duniya ta nuna damuwa cewa matakin zai iya bayar da dama ga Iran da masu ikirarin Jahadi na al-Qaeda da kuma kungiyar IS.
"Shugaban ya kunno wuta ya bar abokansa Larabawa" in ji Elisabeth Marte babbar jami'ar wata cibiya ta tsare-tsare (IISS).
Wani tsohon jami'in dakarun Amurka, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya kwatanta matakin da "wani abu na tarar aradu da ka".
A hukumance, ko da yaushe jagororin kasashen Larabawa na goyon bayan Falasdinawa, tare da la'akari da cewa wannan dadaddiyar magana ce da ta damu ilahirin yankin Larabawa da addinin Islama.
Har yanzu tsofaffin jagororin yankin ba su yi afuwa ga hukumomin Falasdinawa a kan korar Sadam Hussain daga Kuwait a shekarun 1990 ba.
Ba a dade da 'yantar da wannan kasar ba na ga wani wuri a birnin Kuwait an rubuta: "Kudus shi ne gida na din-din-din ga Yahudawa, kuma ni dan Kuwait ne na rubuta haka".
A shekarar 1991 ke nan amma yanzu abubuwa sun sauya.
Yawancin kasashen Larabawa da suke da yawa ba lallai ne su tuna, ko kuma su nuna damuwa da abin da ya faru a 1990 ba. Amma sun damu game da halin da Kudus ke ciki.
Me ya sa aka damu da birnin Kudus?
A Musulunci shi ne wuri na uku mafi tsarki bayan Makka da Madina, kuma yana da daraja da kima a zukatan mutane da dama.
Me hakan yake nufi a wurin masu yaki da ta'addanci? Hakan na nufin akwai hatsari ga bangarori biyu.
Da farko hatsari ne cewar mutanen da a da ba su bayyana kiyayyarsu karara ba ga kasashen yammacin duniya, na iya sauya ra'ayinsu.
Hediya Fathalla wani kwararre ne a fannin tsaron kasashen Larabawa kuma tsohon jami'in gwamnatin Bahrain ya shaida wa BBC cewa, "Akwai masu ra'ayin yin jihadi da suke tunanin "Batun bai kai gareni ba, amma ina jin yin jihadin a raina," ko wannan zai iya ingiza su?
Na biyu shi ne cewa wadanda a baya suna bai wa gwamnatin Amurka hadin kai na iya juya mata baya a sanadiyyar wannan matakin.
Ko a masarautar Saudiyya dole ne yanzu su nuna damuwa cewa Saudiyar ta zabi yin aiki kafada da kafada da Amurka wacce ta fusata yawancin kasashen Larabawa.
Kasar Iran na ci gaba da kokarinta na kwace ikon daga Saudiyya ta fannin iko da martaba a fadin yankin Gabas Ta tsakiya.
Ta dade tana goyon bayan yaki da masu yakar Isra'ila wato 'yan Hezbollah a Labanon da kuma Hamas a yankin Falasdinu.
"Ko da yaushe Iran na amfani da birnin Kudus a matsayin wani dalili na janyo hankalin al'ummar Larabawa, saboda haka ina ganin wannan ma dama ce ga Iran," in ji Hediya Fathalla.
Sharhin da aka samu a shafin ISIS na makon nan, wanda cibiyar ta Manama ta shirya, ya sa Elisabeth Marteu ta yi amannar cewa wannan sanarwar za ta taimaka wa muradun Iran.
Ta kuma rubuta cewa, "wannan zai kara bunkasa martabar Iran wacce take kokarin dawo da martabarta bayan rikicin Syria da Iraki.
Za a dade kafin a iya dinke barakar dangantakar Amurka da kawayenta kasashen Larabawa. Karfi da martabar Amurka da muhimmancinta ba abin da za a iya juya wa baya ba ne.
Sai dai sanarwar da Amurka ta yi ta baya-bayan nan, tunatarwa ce ga shugabannin cewa, har yanzu fadar shugaban Amurka na gasa musu aya a hannu.
Source: BBC Hausa
Title :
Trump Ya Tari Aradu Da Ka
Description : Matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan ayyana Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila ya jawo wa Amurka abin da ya fi suk...
Rating :
5