Kungiyar Hamas ta ce shugaba Donald Trump ya kwanto kura bayan sanarwa da ya yi cewa Amurka ta mayar da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.
Shi dai Mr Trump a lokacin da yake jawabi a fadar White House, ya bayyana matakin a matsayin wani abu da aka dade ba a yi ba a kokarin karfafa zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Shugaban Trump ya ce Amurka za ta goyi bayan masalaha ta hanyar samar da kasashe biyu matukar Israila da Palasdinawa sun amince.
Jim kadan bayan sanarwa Firai Ministan Israila Benjamin Netanyahu ya fito ta gidan talbijin inda ya bayyana matakin a matsayin wani babban abun tarihi.
Mr Netanyahu ya kuma jaddada cewa Israila ba za ta sauya yanayin da ake ciki ba a birnin Kudus wanda ya kunshi wuraren ibada na Yahudawa da Kirista da kuma Musulmai.
Ya ce ''muna matukar godiya ga Shugaban saboda jarumtakarsa da kuma adalar shawarar da ya yanke ta amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila''.
Ya kuma kara cewa shawarar bude ofishin jakadancin Amurka a can alama ce ta kudurin shugaban na yin riko da dadaddiyar gaskiya amma mai dorewa, da cika alkwuran da ya yi, da kuma bunkasa zaman lafiya.
Sai dai kakakin kungiyar Hamas na Palasdinawa ya ce matakin tamkar tsokanar fada ce kawai wanda babu abun da zai haifar illa fitina a yankin.
Shima shugaban kungiyar kwato 'yancin Palasdinawa Saeb Erekat ya ce shugaba Trump ya wargaza masalahar da ake nema ta hanyar samar da kasashe biyu.
Ya ce daga yanzu Amurka ba ta cancanci wani matsayi ba a yunkurin da ake yi na samun zaman lafiya a yankin.
An nasa martanin, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana halin da ake ciki a matsayin zaman zullumi inda ya ce babu wani zabi daya wuce a samar da kasashe biyu.
Source: BBC Hausa
Title :
Trump Ya Kwanto Kura
Description : Kungiyar Hamas ta ce shugaba Donald Trump ya kwanto kura bayan sanarwa da ya yi cewa Amurka ta mayar da birnin Kudus a matsayin babban birni...
Rating :
5