An yanke wa wani dan kasar Ajantina mai 'ya'ya takwas hukuncin shekara 12 a gidan yari.
Wata kotun kasar ta kama Domingo Bulacio mai shekara 57 da laifin yin lalata da 'yar cikinsa har tsawon sama da shekara 20.
'Yar tasa wacce hukuma ba ta bayyana sunanta ba, ta ce ya ajiyeta yana lalata da ita tun lokacin tana 'yar shekara 11.
Al'amarin ya faru ne a garin Villa Balnearia da ke arewacin lardin Santiago del Estero a Ajantina.
Kafofin watsa labaran kasar sun bayar da rahoton cewa mahaifiyar yarinyar (matarsa) ba ta gidan, wata kila ko ta mutu ko kuma ta bar gidan tun lokacin 'yar tana karama.
Gwajin kwayoyin halittar da aka yi ya tabbatar da cewa yarinyar ta haihu da mahaifin nata.
Ta kara da cewa tun daga lokacin da ta bayar da rahoton cin zarafion da mahaifinta yake mata take fuskantar barazanar mutuwa daga danginsu.
An gano lamarin ne a farkon shekarar 2016, lokacin da yarinyar ta je asibiti da daya daga cikin yaran da aka tambayeta tayi bayani game da mahaifinta.
A lokacin da aka kai rahoton wajen 'yan sanda, Bulacio ya tsere inda aka shafe kwana 45 sannan 'yan sanda suka kamo shi suka kuma tsare shi.
Wannan lamari ya yi dai-dai da na Josef Fritzl, wanda aka yanke wa hukunci a shekarar 2009 bisa laifin yin lalata da 'yar cikinsa na sama da shekara 24, a lokacin da ta haifi 'ya'ya bakwai tare da shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Tir:Ankama Uban Daya Shekara 20 Yana Lalata Da Yarsa
Description : An yanke wa wani dan kasar Ajantina mai 'ya'ya takwas hukuncin shekara 12 a gidan yari. Wata kotun kasar ta kama Domingo Bulacio ma...
Rating :
5