Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce goyon bayan da 'yan Nigeria ke nuna masa ita ce babbar garkuwarsa.
Ya bayyana haka ne a wani shirin talbijin da fadar shugaban kasar ta dauki nauyi da aka watsa ranar Lahadi.
Shugaba Buhari ya ce a duk lokacin da ya yi Sallah ya kan gode wa Allah da ya sa talakawa ke matukar kaunarsa kuma suka yarda da shi.
Shirin dai ya tattauna ne da shugaban kasar tare da jin ra'ayoyin wasu fitattun 'yan Najeriya.
Daga cikin su har da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da wasu ministocin gwamnatin wadanda suka yi tsokaci kan halayyar shugaban kasar da kuma salon mulkinsa.
Martani
Wasu masu sharhi a shafukan sada zumunta da muhawara sun yi ta sukar shirin da aka watsa ta gidan talbijin.
Wani dan Jarida mai suna Ja'afar Ja'afar ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa;
".....na kwashe sa'a guda ina bata lokaci wajen kallon shirin da babu komai a ciki illa shirme ..Ban yahewa wallah!
Shi kuwa Idris Mohammed ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa;
''Kasancewar mutane miliyan 12 ne suka zabi shugaba Buhari har yanzu suna goyon bayansa fiye da shekaru goma, babu wani dan siyasa da ya kama kafa sa.. Ko yau aka yi zabe shine zab na."
Sai dai wani mai suna Yakubu Lere cewa ya yi;
''Na fara kallon shirin a matsayina na kwararren ma'aikacin watsa labarai fiye da shekaru 30, amma na ji takaici har sai da na kashe akwatin talbijin d na".....
Wasu dai sun zargi fadar shugaban kasar da neman karkata hankalin 'yan Nigeria game da matsalar karancin mai da ake fuskanta a halin yanzu.
Sai dai mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya mayar da martani ga masu sukar gabatar da shirin a daidai wannan lokaci.
Mr Adesina ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa duk da wahalar karancin mai da ake fuskanta na kankanen lokaci, ya zama wajibi a waiwayi wani batu mai farantawa al'umma rai.
Wasu masu lura da al'amura a Najeriyar dai na ganin wannan shiri tamkar sharar fage ne kan shirye shiryen shugaba Buhari na sake tsaya wa takarar 2019.
Sai dai kawo yanzu shugaba Buhari bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Talakawa Na Matukar Kaunata-Buhari
Description : Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce goyon bayan da 'yan Nigeria ke nuna masa ita ce babbar garkuwarsa. Ya bayyana haka ne a wani sh...
Rating :
5