Gwamnatin Switzerland ta ce za ta mayar wa Najeriya dala miliyan 320 (Fam miliyan 240) daga cikin kudaden da ake zargin cewa tsohon shugaban mulkin soja Sani Abacha ya sace.
Wata kotun Switzerland ce ta hana amfani da kudin a shekarar 2014 bayan an fara shari'a akan dan marigayin Abba Abacha.
Kudin da aka fara ajiye wa a birnin Luxembourg, kadan ne daga biliyoyin dalolin da ake zargin an sace a lokacin mulkin Sani Abacha tsakanin 1993 zuwa 1998.
"Kwato kudin da Abacha ya sace" ya kasance daya daga cikin alkawuran da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a lokacin yakin neman zabe a shekarar 2015.
Kuma wannan zai kasance kudi mafi yawa da aka kwato kawo yanzu.
An dai rattaba hannun kan yarjejeniyar mayar da kudin tun a watan Maris na 2015.
Sai dai ma'aikatar shari'ar kasar da bankin duniya da kuma lauyoyi daga Switzerland da Amurka sun yi ta fama sarkakiyar da ke tattare da mayar da kudin-in ji wakiliyar BBC Stephanie Hegarty.
A ranar Litinin kasar Switzerland ta sanar da cewa an shawo kan matsalar kuma za a mayar wa gwamnatin Nigeria da kudin.
Koda yake ba ta fayyace lokacin da za a mayar da kudin ba, amma ta ce wajibi bankin duniya ya sa ido kan yadda za a kashe kudin, don tabbatar da cewa an yi amfani da su "domin jin dadin 'yan Najeriyar".
"Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da Switzerland ta ba muhimmanci" in ji ministan harkokin wajen kasar Didier Burkhalter.
Ministar ta kara da cewa yunkurin zai "inganta rayuwar 'yan Najeriya da ke fama da matsanancin talauci ", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Source: BBC Hausa
Title :
Switzerland Zata Mayar Wa Nijeriya Makudan Kudin Da Ake Zaton Abacha Ya Sata
Description : Gwamnatin Switzerland ta ce za ta mayar wa Najeriya dala miliyan 320 (Fam miliyan 240) daga cikin kudaden da ake zargin cewa tsohon shugaban...
Rating :
5