Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile wani hari da 'yan kungiyar BokoHaram su ka yi yunkurin kai wa a birnin Maiduguri a ranar Kirsimeti.
Kwamandan rundunar sojojin ta Lafiya Dole a yankin arewa maso gabashin kasar Major Janar Nicholas Rogers shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa.
Ya ce dakarun sojin sun yi bata kashi da masu tayar da kayar bayan da suka farma wani wurin binciken ababen hawa na sojoji da ke wajen birnin a cikin motocin a kori kura.
Janar Nicholas Rogers ya ce an kwashe sama da awa guda ana artabu tsakanin mayakan da sojoji.
Sanarwar ta ce babu asarar rayuka sai dai a lokacin da maharan ke tserewa sun kona wasu motoci biyu da wasu gidaje da ke kusa.
Hukumomi a birnin Maiduguri sun ce an kara tsaurara matakan tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Source: BBC Hausa
Title :
Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Maiduguri
Description : Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile wani hari da 'yan kungiyar BokoHaram su ka yi yunkurin kai wa a birnin Maiduguri a ranar Kirsime...
Rating :
5