Kotun daukaka kara ta yankin Abuja ta tasa keyar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, zuwa kotun da'ar ma'aikata domin a sake masa sharia kan zargin rashin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa.
Gwamnatin Najeriya dai ta daukaka kara ne bayan kotun da'ar ma'aikata ta wanke shugaban majalisar dattawan Najeriyar da farkon wannan shekarar.
Kotun da'ar ma'aikatar ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume 18 na rashin fadin gaskiya wajen bayyana kadarori da aka yi wa Saraki.
A zamanta a yau, kotun ta yanke hukuncin cewa Mista Saraki bai bayar da gamsasshiyar amsa kan uku daga cikin tuhume-tuhume 18 da aka masa ba.
Masu shari'ar uku da suka jagorancin zaman kotun karkashin alkali Tinuade Akomolafe-Wilson, sun yi watsi da sauran tuhume-tuhume 15 din da gwamantin Najeriyar ta yi wa Saraki.
Sai dai kuma wata sanarwa daga ofishin watsa labaran Bukola Saraki ta ce shugaban majalisar dattawan Najeriyar zai daukaka kara kan hukuncin.
Shi kuwa lauyan gwamnatin Najeriya kan shari'ar, Rotimi Jacobs, ya ce zai yi nazari kan hukuncin kotun kafin ya yanke shawara kan matakin da zai dauka.
Source: BBC Hausa
Title :
Saraki Zai Sake Shiga Kotu
Description : Kotun daukaka kara ta yankin Abuja ta tasa keyar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, zuwa kotun da'ar ma'aikata dom...
Rating :
5