Wani rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a garin Bwari da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Rikicin dai ya barke ne bayan wasu da aka ce 'yan kungiyar asiri ne suka kai wani hari ranar Lahadi da daddare.
Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa harin ya yi sanadin mutuwar wani mutum.
Duk da cewar rikicin kamar ya kwanta daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin, amma ya sake dawowa a ranar Litinin din inda aka yi ta afka wa juna tsakanin 'yan kabilar Gbagi (Gwarii) da Hausawa.
Wani mazaunin Bwari ya shaida wa BBC cewa an kona kusan rabin kasuwar Bwari.
Kasuwar kamar wata matattara ce inda kabilu daban-daban mafi yawa Hausawa da Igbo ke kasuwanci.
Rundunar 'yan sanda a birnin Abuja ta tabbatar wa BBC cewa tuni ta tura jami'anta a garin na Bwari domin kwantar da rikicin.
Sai dai kakakin rundunar, Anjuguri Jesse Manzah, bai yi karin haske a kan adadin rayuka da kadarori da suka salwanta ba, yana mai cewa rundunar ta fi mayar hankali ne kan kokarin tabbatar da doka da oda kafin ta fara kididdigar abubuwan da aka rasa.
Kawo yanzu dai ba a san ainihin dalilin da ya kawo barkerwar wannan rikici ba, wanda kafin barkewar sa, mazauna yankin ke cewa ana zaune lafiya tsakanin kabilun da ke rayuwa a garin.
Source: BBC Hausa
Title :
Rikicin Kabilanci Ya Barke A Wani Yankin Abuja
Description : Wani rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a garin Bwari da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Rikicin dai ya barke ne bayan wasu da aka...
Rating :
5