Rahotanni daga jihar Adamawan Najeriya na cewa wani rikici mai nasaba da kabilanci da kuma rikicin gonaki ya barke a kauyukan da ke kusa da garin Numan, lamarin da ya hana masu tafiya wucewa tare da tilasta wa wasu kauracewa daga garin Numan.
Kauyukan da aka kai wa hare-haren sun hada da Bono da Laworu da Dom, duka a kusa da garin Numan.
Wasu shaidu sun shaida wa BBC cewa an kona kauyukan kurmus ne, inda ita kuma gwamnatin jihar Adamawa take cewa an tafka barna a cikin a kalla biyu daga cikin kauyuka.
Shaidun dai sun ce makiyaya ne suka kai hare-haren kan kauyukan a wani mataki na rama harin da aka kai musu makonni biyu da suka gabata, inda aka kashe yara da mata.
Wani mazaunin Numan da ya arce Yola saboda rikicin, Sanusi Sani Saleh, ya ce an dade ana zaman dar-dar saboda tsoron barkewar rikicin.
Ya ce duk da cewa akwai jami'an tsaro a cikin garin na Numan, yana ganin rikicin ya fi karfinsu yana mai neman gwamnati ta kai musu dauki.
Kwamishinan watsa labaran jihar Adamawa, Ahmed Sajo, ya tabbatar wa da BBC cewa an yi barna a kauyukan Laworu da Dom da ke kusa da garin Numan, yana mai cewa hankali ya kwanta a cikin garin na Numan.
Ya ce an tura karin sojojin sama da 'yan sanda suna shawagi a jiragen yaki a sararin samaniyar garin Numan domin ganin an shawo kan matsalar.
Kwamishinan, wanda ya alakanta rikicin da rashin yafiya da akew samu tsakanin kabilu, ya ce gwamnatin jihar tana kokarin binciken harin da aka kai wa makiyaya a baya, amma hakan na bukatar bincike sosai don samun masu laifi kafin ta hukunta su.
Kwanan nan ne dai aka kashe wasu 'yan sanda da suka je neman kwato makamai daga wasu 'makiyaya' a yankin na Numan.
Rikicin makiyaya da manoma dai wani rikici ne da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Rikicin Kabilanci Ya Barke A Jihar Adamawa
Description : Rahotanni daga jihar Adamawan Najeriya na cewa wani rikici mai nasaba da kabilanci da kuma rikicin gonaki ya barke a kauyukan da ke kusa da ...
Rating :
5