Gwamnatin Najeriya, ta bullo da wani tsari domin magance tashe-tashen hankulan da ake fama da su tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma a wasu yankuna na kasar.
A ranar litinin din data gabata ne mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya tattauna da wasu masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin magance matsalar.
Mai martaba sarki Kano, Muhammadu Sanusi na II da kuma Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu, na daga cikin wadanda suka halarci taron, baya ga wasu shugabannin fulani.
Dr Aliyu Tilde na daga cikin wadanda suka halarci taron, ya kuma shaida wa BBC cewa, an tattauna matsalolin da suka kunno kai a baya-bayan nan wadanda suka shafi tashen-tashen hankulan da ake samu tsakanin fulani makiyaya da manoma.
Dr Tilde, ya ce an tattaunawar an fito baro-baro an shaida wa mataimakin shugaban kasa irin matsalollin da makiyaya ke ciki.
Ya ce, matsaloli na kin bin doka da kuma barin abubuwa su lalace ba tare da daukar matakin da ya da ce a kai ba suke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Dr Tilde, ya ce yakamata yanzu makiyaya su sani cewa ana kokari ayi nazari a kan matsalolinsu da kuma lalubo hanyar magance su.
A makon da ya gabata ne mataimakin shugaban Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci garin Numan na jihar Adamawa bayan hare-hare da aka kai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Kazalika ko a watan Nuwamban 2017 ma, rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a yankin tsakanin kabilun Bacama da Fulani inda aka kashe mutane akalla 20.
Source: BBC Hausa