Dan wasan tsakiya na Faransa Corentin Tolisso ya daga ragar PSG sau biyu Bayern Munich ta yi nasarar doke PSG 3-1, amma kuma 'yan Faransan sun kai matakin 'yan 16 a matsayin na daya a rukuninsu na gasar zakarun Turai.
Bayern na bukatar ta doke zakarun Faransan da kwallo hudu kafin ta zama ta daya a rukunin na biyu, (Group B).
Robert Lewandowski ne ya fara ci wa zakarun na Jamus bayan minti takwas da shiga fili, sai kuma Tolisso ya biyo baya da ta biyua a minti na 37 da kuma ta uku a minti na 69.
To amma kafin Tolisso ya ci ta uku, bayan ya zura ta biyu, ana 2-0 Kylian Mbappe ya ci wa bakin bal dinsu daya tilo a minti na 50.
A ranar Litinin mai zuwa ne za a hada jadawalin wasannin gaba na gasar ta zakarun Turai a hedikwatar hukumar kwalllon kafa ta Turai Uefa a birnin Nyon na Switzerland.
A rukuni na biyu (Group B) kuwa Celtic ta kammala wasanninta na rukuni a matsayin ta uku, kuma ta samu damar zuwa gasar Europa duk da rashin nasarar da ta yi a gidanta a hannun Anderlecht 1-0.
Source: BBC Hausa
Title :
PSG Tasha Kashi A Gun Bayern Daci 3 da 1
Description : Dan wasan tsakiya na Faransa Corentin Tolisso ya daga ragar PSG sau biyu Bayern Munich ta yi nasarar doke PSG 3-1, amma kuma 'yan Farans...
Rating :
5