Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta tura wata tawaga wadda zata zagaya sassan Nigeria domin ta bai wa 'ya yanta da suka yi fushi hakuri dangane da zaben shugabanninta da aka yi ranar Asabar.
Ta dauki wannan matakin ne bayan da wasu 'ya yanta suka nuna rashin jin dadinsu dangane da zaben.
Tun kafin a kammala zaben dai 'yan takara shugabancin jami'yyar da dama ne suke janye takararsu don nuna adawa da yadda zaben ya gudana kuma har yanzu ake ci gaba da kace-nace a kansa.
Wasu 'ya yan jamiyar sun rika tada jijiyar wuya bayan da aka bayana sakamakon zaben.
Wasu daga cikinsu sun nemi jam'iyyar ta mayar musu da kudin fom dinsu saboda a cewarsu ba a yi adalci a zaben ba.
Yan takarar dai sun nuna rashin jin dadinsu game da wata takarda mai dauke da jerin sunnayen wasu da aka ce sune sabbin shugabannin jam'iyyar da aka kira Unity list, da aka rika rarabawa tun kafin a kamala zaben.
Sai dai kwamitin da aka dorawa alhakin shirya zaben ya musanta cewa an yi magudi a zaben.
Sakataren watsa labarai na kwamitin, John Odey ya ce jam'iyyar ta dauki wasu matakan rage 'yan takara ne saboda yawansu ya wuce kima
Wasu masana harkokin siyasar Nigeria ,sun ce har yanzu jam'iyyar hamayya ta PDP ba ta koyi darasi ba, tun zaben da ta sha kaye a shekarar 2015.
Source: BBC Hausa
Title :
PDP Na Rarrashin Ya'yanta Dasuka Fusata
Description : Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta tura wata tawaga wadda zata zagaya sassan Nigeria domin ta bai wa 'ya yanta da suka yi fushi hakuri...
Rating :
5