Tsohonshugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi gargadi a kan amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ta yadda ya dace ba, a wata hira da ba safai yakan yi ba tunda ya sauka daga mulki a watan Janairu.
Ya ce yin amfani da shafukan ba yadda ya dace ba yana gurbata tunanin mutane kan al'amura masu sarkakiya, da kuma yada labaran karairayi.
Mutumin da ya gaje shi, Donald Trump, ya shahara wurin yin amfani da Twitter, ko da yake Mr Obama bai ambaci sunansa a hirar ba.
Yarima Harry ne ya yi hira da tsohon shugaban kasar a madadin shirin Radio 4 na BBC.
Yariman, wanda shi ne na biyar a cikin jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniya, na cikin masu gudanar da shirye-shirye a shirin Radio 4 tsawon lokacin bukuwan Kirsimeti.
Tsohon shugaban kasar ya kuma bukaci masu rike da madafun iko su rika yin takatsantsan kan irin sakonnin da suke wallafawa a shafukan zumunta, yana mai cewa shafukan na kawo matsala game da rayuwar jama'a.
Mr Obama ya bayyana taiakcinsa kan yadda ake maye gurbin labarai na gaskiya da labaran kanzon-kurege, da kuma yadda mutane ke karanta ko saurarar abin da kawai zai gamsar da ra'ayinsu ba tare da tantance sahihancinsa ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Obama Yayi Gargadi Kan Amfani Da Shafukan Sada Zumunta
Description : Tsohonshugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi gargadi a kan amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ta yadda ya dace ba, a wata hira d...
Rating :
5