Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari game da nade-naden mutanen da tuni suka mutu a mukamai na hukumomin gwamnati.
Jam'iyyar PDP ta ce wannan ya zama babban abin kunya ga Najeriya a karkashin jagorancin jam'iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya sanya wa hannu, PDP ta ce gwamnatin APC ta gaza.
"Gwamnatin APC ta rikice baki daya, ta yamutse, kuma a fili yake cewa ba zata iya tafiyar da mulkin kasar ba idan aka lura da irin rikon sakainar kashi da gwamnatin APC ke yi wa lamuran kasar."
Amma kakakin gwamnatin Najeriya, Garba Shehu ya kare wannan lamarin, inda ya ce tsohon jadawali ne da ya dade yana jiran shugaban kasa ya amince da shi:
"Tun watan Oktobar shekarar 2016 aka rubuta sunayen wadanda aka nada. Amma sai aka ajiye shi domin sukar da wasu gwamnoni suka yi."
Ya ce daga baya shugaba Buhari ya bada umarnin a saki sunayen cikin kurarren lokaci, wanda a ganinsa ya janyo wannan matsalar.
Ya kuma tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnati zata sauya sunayen wadanda suka mutun da wasu wadanda suka cancanta.
A nata bangaren, jam'iyyar ta PDP ta ce wannan batu ya nuna dalilan da suka sa tattalin arzikin kasar ya kasa farfadowa.
"Yaya gwamnatin da bata iya shirya jadawalin ma'aikata ba zata iya fuskantar manyan ayyukan kasa kamar shirya kasafin kudin kasa, da tsare-tsaren ayyukan ci gaban kasa da batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da ilimi da noma da kuma sarrafa ma'aikatan gwamnati?"
Sanarwar ta PDP ta kara da cewa: "Gaskiyar magana ita ce kasarmu ta shiga hannayen wadanda basu san ina suka dosa ba a shekaru biyun da suka gabata."
Ta ce tana tsoron makomar kasar, daga yanzu zuwa shekara ta 2019.
Kakakin gwamnati, Garba Shehu ya cigaba da kareta, kuma ce bai ga dalilin da za a hukunta wani jami'in gwamnati ba dangane da wannan lamarin.
Source:BBC Hausa
Title :
Nada Matattu A Gwamnatin Buhari Rashin Iya Aiki Ne-PDP
Description : Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari game da nade-naden mutanen da tuni suka mutu a mukamai n...
Rating :
5