Ministan Shari'ar Najeriya Barista Abubakar Malami ya ce za su roki Shugaban Kasar Muhammadu Buhari don ya sake tsayawa takara a babban zaben kasar wanda za a yi a shekarar 2019.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kawo mana a ofishinmu na Landan kwanakin baya.
Sai dai babban lauyan gwamatin kasar ya ce shugaban bai sanar da su matsayinsa a kan hakan ba tukuna.
Haka zalika ya ce su a shirye suke su "roke shi da ya sake tsayawa takarar saboda ganin abubuwa na alkairi da shugaban ya faro a kasar sun wanzu."
Yayin da aka tambayi ministan ko zai amsa kiran nasu, ganin cewa su mukarrabansa ne.
Sai ya kada baki ya ce "za mu tsananta roko."
Game da batun talauci da al'ummar ke fama shi kuwa, ministan ya ce abubuwa suna "kyautatuwa" ganin yadda kasar ta fara yin karfi a bangaren noma.
Har ila yau ya bayyana cewa an samu ci gaba ta fuskar tsaro, inda ya ce "a baya ma ai ba batun talauci ake yi, batun rayuwa ake yi."
Source: BBC Hausa
Title :
Muzamu Roki Buhari Yayi Takara 2019-Malami
Description : Ministan Shari'ar Najeriya Barista Abubakar Malami ya ce za su roki Shugaban Kasar Muhammadu Buhari don ya sake tsayawa takara a babban ...
Rating :
5