Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce mutum miliyan uku ne suka rasa aiki a lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Facebook ranar Lahadi.
Atiku Abubakar ya ce "gwamnatin APC ta yi alkawarin samar wa mutum miliyan uku aiki a kowaccce shekara amma mutum miliyan ukun ne suka rasa aikinsu a lokacinta".
A cewarsa, ya fitar daga APC ne inda ya koma PDP saboda matsalolin da suka sa ya fice daga PDP a shekarar 2014 "an warware su yanzu."
Sai dai bai fito fili ya bayyana anniyarsa ta sake neman shugabancin kasar a babban zaben kasar na shekarar 2019.
Ya ce ya koma jam'iyyar ne saboda matsalolin da suka sa ya fice daga PDP a shekarar 2014 "an warware su yanzu."
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari gwamnatin Shugaba Buharin ba ta mayar da martani ba.
Amma a baya sun sha yin watsi da wasu zarge-zargen da Atikun ya sha yi kan jam'iyyar APC da ma mulkin Shugaba Buhari.
Har ila yau tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce jam'iyyar APC ta "kasa cika alkawurran da ta yi wa al'ummar kasar musamman matasa."
A cikin watan jiya ne ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.
A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauya jam'iyyun siyasa. Kuma wannan ne karo na biyu da dan siyasar yake koma wa jam'iyyar PDP.
Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban Najeriya ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
A shekarar 2007 ne ya fara tsakayawa takarar shugabancin Najeriya ne a karkashin jam'iyyar AC.
Hakazalika ya sake neman takarar a shekarar 2011, amma bai samu tikitin jam'iyyarsa ta PDP ba.
Atiku Abubakar ya kara neman tsayawa a shekarar 2014, inda a nan ma bai samu tikitin shugabanci ba a karkashin jam'iyyar APC.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutum Miliyan Uku Ne Suka Rasa Aiki A Mulkin Buhari-Atiku
Description : Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce mutum miliyan uku ne suka rasa aiki a lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu B...
Rating :
5