Kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa wato kwalara, ya kai miliyan guda a Yemen .
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Geneva, ta bayyana adadin a matsayin abin damuwa.
Red Cross ta ce, kaso 80 cikin 100 na mutanen kasar na fama da karancin abinci da man fetir da tsaftataccen ruwan sha da kuma magunguna.
Kasar Yemen dai na cikin yakin basasa tsakanin dakarun kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta da kuma 'yan tawayen Houthi wadanda ke samun goyon bayan Iran.
Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar ta kwalara na karuwa a kowacce rana a Yemen, kuma a iya cewa kusan ba bu wani taimako da za a iya yi don yi wa wadanda suka kamu da cutar magani.
Rufe tashoshin ruwan Yemen da kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta ya yi, koda yake an dan bude su, na sa har yanzu ana samun jinkiri wajen isar magunguna cikin kasar.
Ba a shigar da man fetir kasar, ga karancin ruwan sha inda cibiyoyin da ke samar da ruwa a kasar ba sa aiki yadda yakamata ko kuma ba bu su ma kwata-kwata.
Abinci ba bu, yara na fama da rashin abinci mai gina jiki wanda hakan ke sa ba sa iya jurewa duk wata cuta da ta shige su.
Kasar Yemen dai, ita ce kasar da ta fi fama da matsalar ayyukan jin kai a duniya.
Hukumomin agajin da suke kai mata dauki sun ce hakan nada nasaba da tashin hankalin da ake fama dashi a kowacce rana a kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutum Miliyan Guda Nafama Da Kwalara A Yemen
Description : Kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa wato kwalara, ya kai miliyan guda a Yemen . A cikin wat...
Rating :
5