Yan sanda a jihar Madhya Pradesh da ke Indiya na neman ministan ma'aikatar sanya farin ciki ruwa a jallo saboda zargin yin kisa.
'Yan sandan sun ce suna farautar Lal Singh Arya, mai shekara 53, wanda ba a gani ba tun ranar Talata bayan kotu ta bayar da umarnin tsare shi.
Ana zarginsa da kashe wata 'yar siyasa a shekarar 2009 ko da yake a baya ya sha musanta zargi.
Madhya Pradesh ita ce jihar da kawai take da ministan farin ciki da zummar kula da walwalar jama'a.
Gwamnatin da jam'iyyar Bharatiya Janatake jagoranta ce ta kirkiro da ma'aikatar a shekarar 2016 sannan ta dora mata alhakin "tabbatar da farin ciki da walwalar 'yan kasar".
Madhya Pradesh, ita ce jiha ta biyu mafi girma a Indiya, inda take da kimanin mutum miliyan 7 .
Mr Arya, wanda shi ne mutumin da ke shugabancin ma'aikatar tun da aka bude ta, yana kuma jagorantar ma'aikatu biyu, ciki har da na safarar jiragen sama da gudanarwa da walwalar kabilu.
Ana sa ran zai gurfana a gaban kotu ranar 19 ga watan Disamba.
"'Yan sanda suna nemansa. Muna da kwarin gwiwar cewa za mu kama shi," in ji wani dan sanda a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Source: BBC Hausa