Yan Najeriya da dama na ci gaba da fuskantar karancin man fetur duk da umarnin da gwamnati bai wa ministan man fetur na ya tabbatar an kawo karshen matsalar.
A ranar Larabar makon jiya ne ministan watsa labarai Lai Mohammed ya yi wa 'yan jarida bayani bayan taron Majalisar Ministoci cewa an umarci takwaransa na harkokin mai, Ibe Kachikwu ya gaggauta kawo karshen matsalar ta man fetur kafin karshen makon jiya.
A wancan lokacin, kakakin babban kamfanin mai na kasa, NNPC, Ndu Ughamadu, ya bayyana kwarin gwiwarsa ta kawo karshen matsalar.
Sai dai mutanen da muka yi magana da su a jihodi da dama na Najeriya ranar Talata sun ce suna ci gaba da fuskantar wannan matsala.
Mallam Ibrahim Adamu wani direban motar haya a jihar Kano ya ce "babu wata alama da ke nuna cewa za a kawo karshen wannan matsala nan kusa".
"Hasalima tun daga ranar da aka ce za a shawo kan wannan matsala, mu a Kano kamari take dada yi", in ji shi.
Wannan kalami na Mallam Ibrahim shi ne kusan abin da dukkan mutanen da BBC ta tuntuba ke cewa.
Hakan ya sa masu sayar da fetur a kasuwar fage ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin kamfanin mai na NNPC kan abin da ya sa ake ci gaba da fama da karancin fetur duk da umarnin da gwamnati ta bayar kan magance shi amma ba mu yi nasara ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Meyasa Baa Daina Wahalar Man Fetur A Nijeriya Ba?
Description : Yan Najeriya da dama na ci gaba da fuskantar karancin man fetur duk da umarnin da gwamnati bai wa ministan man fetur na ya tabbatar an kawo ...
Rating :
5