Barcelona za ta ziyarci Real Madrid a gasar cin kofin La Ligar Spaniya wasan mako na 17 a Santiago Bernabeu a ranar Asabar.
Wannan ne karo na hudu da kungiyoyin biyu masu buga wasan hamayya da ake masa lakabi da El Clasico za su kece - raini a kakar wasan shekarar nan.
Real Madrid da Barcelona sun yi fafata a gasar International Champions Cup a Amurka a ranar 30 ga watan Yuli, inda Barca ta yi nasarar cin Real 3-2.
A ranar 13 ga watan Agusta ne Barca ta yi rashin nasara da ci 3-1 a hannun Real a Super Cup wasan farko, a wasa na biyu Real ce ta doke Barca da ci 2-0 a Santiago Bernabeu.
Real Madrid mai rike da kofin Zakarun nahiyoyin duniya wacce take da kwantan wasan La Liga daya, tana ta hudu a kan teburin gasar da maki 31.
Ita kuwa Barcelona tana mataki na daya ne a kan teburi da maki 42 bayan da ta yi wasa 16.
Source: BBC Hausa
Title :
Messi Zai Ziyarci Bernabeu A Wasan El-Classico
Description : Barcelona za ta ziyarci Real Madrid a gasar cin kofin La Ligar Spaniya wasan mako na 17 a Santiago Bernabeu a ranar Asabar. Wannan ne karo ...
Rating :
5