A karon farko tun 2014 Manchester United ta kai matakin wasan sili-daya-kwale na kofin gasar zakarun Turai bayan da ta farfado ta doke CSKA Moscow 2-1.
Nasarar ta United a Old Trafford ta ba wa kungiyar ta Jose Mourinho damar zama ta daya a rukuninsu na farko (Group A) a gaban ta biyu Basel da maki 15 a wasa shida.
Ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ne kungiyar ta Rasha ta ci bal din da ake ganin akwai satar gida, bayan da Vitinho ya sheko bal din ta taba bayan Alan Dzagoev, wanda yake shi kadai a wurin ta kauce ta shiga raga.
Bayan an dawo wasa ne a minti na 64 Romelu Lukaku ya rama ta farko bayan da Pogba ya saita masa bal din wadda ta zama ta 13 da ya ci a kakar nan. Minti biyu tsakani ne kuma sai Rashford ya ci ta biyu.
Yanzu Man United za ta iya haduwa da daya daga cikin wadannan a matakin na gaba na sili-daya-kwale; masu rike da kofi Real Madrid ko Bayern Munich da ta dauki kofin sau biyar ko kuma zakarun Italiya Juventus.
Nasarar kuma ta sa yanzu United ta yi wasa 40 da ba a doke ta ba a gidanta Old Trafford, a dukkanin gasar da take yi.
Source: BBC Hausa
Title :
Man United Ta Doke CSK Moscow Daci 2 da 1
Description : A karon farko tun 2014 Manchester United ta kai matakin wasan sili-daya-kwale na kofin gasar zakarun Turai bayan da ta farfado ta doke CSKA ...
Rating :
5