Majalisar tabbatar da shari'ar musulunci a Najeriya ta soki lamirin Shugaban kasar Muhammadu Buhari, saboda rashin halartar taron kungiyar kasashe musulmi ko kuma OIC a kasar Turkiyya.
Taron dai wanda aka yi a kasar Turkiyya ya yi Allah wadai da matakin Amurka na daukar Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.
Babban sakataren kungiyar Malam Nafi'u Baba-Ahmed, ya shaida wa BBC cewa matsayar da suka dauka ita ce za su yi kokarin ganawa da Shugaba Buhari don su nuna masa cewa ba a yi musu adalci.
Ya ce: "A yanzu haka babu abun da musulmai suka fi mayar da hankali a kai irin rikicin Kudus, an kira dukkanin shugabannin kasashen musulmai wanda Najeriya tana ciki, amma sai ya yi tafiyarsa Faransa taron sauyin yanayi.
"Wanne ya fi muhimmanci tsakanin biyun? Mafi yawan 'yan Najeriya musulmai ne kuma mafi yawan wadanda suka zabe shi musulmai ne, abun nan kuma ya dame su, da ya je ai da ya share musu hawaye," in ji Malam Nafi'u Baba-Ahmed.
Malam Nafi'u ya kara da cewa a yanzu duk wani musulmi ya kullaci Shugaba Buhari kan wannan lamarin.
Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin bangaren shugaban kasa kan wannan sukar amma har zuwa lokacin wallafa labarin ba mu yi katarin samunsu ba.
A ranar 13 ga watan Disamba ne kungiyar hadin kan musulmai ta OIC ta yi taro na musamman kan rikicin da ya kunno kai kan mayar da Kudus babban birnin Isra'ila da Amurka ta yi a baya-bayan nan.
Mafi yawan shugabannin kasashen musulmai na kungiyar sun halarci taron.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar tasa da Mukhtari Adamu Bawa na BBC:
Source: BBC Hausa
Title :
Majalisar Shari'ah Tasoki Buhari Kan Kin Zuwa Taron OIC
Description : Majalisar tabbatar da shari'ar musulunci a Najeriya ta soki lamirin Shugaban kasar Muhammadu Buhari, saboda rashin halartar taron kungiy...
Rating :
5