Kamfanin jirgin sama na Cathay Pacific ya ce ma'aikatansa sun ga giftawar abun da suka yi amannar cewa makami mai linzamin da Koriya Ta Arewa ta harba ne a makon jiya, yayin da jirgin ke bi ta sararin samaniyar kasar Japan.
Kamfanin jirgin ya tabbatar wa da BBC cewa ma'aikatansa sun ga abun da suka yi tsammanin cewa sake shigar makami mai linzamin ne cikin sararin samaniya.
Ya kara da cewa a halin yanzu dai ba a sauya hanyar da jirage ke bi ba.
A ranar 29 ga watan Nuwamba ne Koriya Ta Arewa ta sake harba wani sabon makami mai linzaminta da ta ce zai iya kai wa isa ko ina a Amurka.
Kaddamar da harin ya sake tayar da sa-in-sar da dama can ke tsakanin kasar da Amurka da kuma makwabciyarta Koriya Ta Kudu, inda aranar Litinin din makon da ya gabata suka fara wani atisayen soji na hadin gwiwa.
Makamin ya tarwatse a sararin samaniya
Harin da Koriya Ta Arewan ta kai wanda ta bayyana a matsayin mafi karfi da ta taba kai wa, ya sauka ne a tekun kasar Japan, sai dai a wannan karon ya wuce inda ya saba kai wa.
Jaridar South China Morning Post ta ce manajan kamfanin jirgi na Cathay Mark Hoey, ya shaida wa ma'aikatansa cewa: "A yau ma'aikatan da ke cikin jirginmu mai lamba CX893, sun bayar da rahoton cewa sun ga tarwatsewar makami mai linzamin Koriya Ta Arewa a kusa da inda jirginsu ke tafiya."
Haka kuma wasu jiragen Koriya Ta Kudu biyu ma da suke kan hanyarsu ta zuwa babban birnin kasar Seoul daga Amurka sun ce sun ga giftawar makamin.
Ba kamar sauran kasashe ba, Koriya Ta Arewa ba ta bayar da sanarwa idan za ta yi gwajin makami mai linzami, wanda hakan ke nufin cewa akwai yiwuwar ya bi ta hanyar jiragen sama, kuma hakan hatsari ne babba.
Sai dai Koriya Ta Arewan tana da bayanan hukumar zirga-zirgar jiragen sama, don haka za ta iya sanin ya ya yanayin hanyoyin sararin samaniyar suke kafin su kaddamar da hari.
Sai dai duk da cewa barazanar ba ta da yawa, to jiragen sama na bukatar yin taka-tsan-tsan da kuma lura.
A farkon watan Agusta ne, kamfanin jirage na kasar Faransa ya fadada yankin da ya haramta wucewar jiragensa a yankin samaniyar Koriya Ta Arewa, bayan da ta bayyana cewa daya daga cikin jiragensa ya bi ta dab da hanyar da makami mai linzamin Koriyan ke bi.
Atisayen hadin gwiwa da sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudun suke yi zai kai tsawon kwana biyar.
Za a yi amfani da jiragen yaki 230 da kuma dubun-dubatar dakaru.
Sai dai Koriya Ta Arewa ta soki al'amarin, inda a karshen mako ta ce Amurka na son a yi yakin makami mai linzami, kuma za ta dauki mataki kan atisayen da take yi din.
Source: BBC Hausa
Title :
Ma'aikatan Jirgin Sama Sunga Giftawar Makami Mai Linzamin Koriya Ta Arewa
Description : Kamfanin jirgin sama na Cathay Pacific ya ce ma'aikatansa sun ga giftawar abun da suka yi amannar cewa makami mai linzamin da Koriya Ta ...
Rating :
5